Ganduje ya bude ma Atiku dandanlin da zai gudanar da gangamin yakin neman zabe

Ganduje ya bude ma Atiku dandanlin da zai gudanar da gangamin yakin neman zabe

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya janye umarnin daya bayar na farko inda ya bukaci a garkame filin wasa na tunawa da Sani Abacha dake Kano, wanda Atiku Abubakar yaso ya yi amfani dashi wajen gangamin yakin neman zabensa.

Atiku Abubakar shine dan takarar shugabancin Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP, kuma a ranar Lahadi, 10 ga watan Feburairu ake sa ran zai shiga jahar Kano domin gudanar da yakin neman zabensa, jahar da ake ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari na da karfi sosai.

KU KARANTA: PDP ta nemi kasashen Amurka da Birtaniya dasu dauki tsatstsauran mataki akan El-Rufai

Ganduje ya bude ma Atiku dandanlin da zai gudanar da gangamin yakin neman zabe

Ganduje Atiku
Source: UGC

A dalilin haka ne kwamitin yakin neman zaben Atiku ta nemi a bata filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata domin shirya gangaminta, sai dai gwamnan jahar Kano Ganduje ya hana, inda ya bada umarnin a garkame filin wasan domin gudanar da gyare gyare.

A yayin da gwamnatin jahar ta bayyana cewa ta rufe filin domin gudanar da wasu gyare gyare ne, sai aka jiyo kaakakin hukumar wasanni ta jahar Kano, Abbati Sabo yana cewa an garkame filin ne saboda kakar wasan gasar firimiya ta Najeriya.

Sai dai a wani mataki na yin amai da lashewa, kwamishinan watsa labaru na jahar Kano, Muhamamd Garba ya bayyana cewa gwamnati ta umarci dan kwangilan dake gudanar da aikace aikacen daya kwashe kayan aikinsa gaba daya domin baiwa Atiku Abubakar damar gudanar da gangaminsa.

“A matsayinsa na cikakken dan dimukradiyya, wanda ya amince da yancin tarayya da mu’amala, gwamnan jahar Kano Abdullahi Ganduje bait aba bada umarnin a kulle filin wasa na Sani Abacha da nufin musguna ma jam’iyyar PDP ba, an kulleta ne kawai domin gudanar da aikace aikace.

“Daga karshe muna yi ma PDP fatan gudanar da gangaminsu cikin lafiya da kwanciyar hankali, a tashi dan kallo lafiya dan wasa ma lafiya, haka zalika muna kira ga shuwagabannin PDP dasu tabbata mabiyansu sun bi doka da oda a yayin taron, ba tare da sun lalata komai a filin ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel