Gwamnati da Malamai zasu goga gemu da gemu a zama na karshe dangane da yajin aiki

Gwamnati da Malamai zasu goga gemu da gemu a zama na karshe dangane da yajin aiki

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a yau Alhamis, 7 ga watan Feburairu ne za ta koma bisa teburin sulhu tsakaninta da kungiyar malaman jami’a da suka tubure sai an biya musu bukatunsu kafin su koma bakin aiki tun bayan kaddamar da yajin aiki.

Ministan kwadago, Chris Ngige ne ya bayyana haka a ranar Laraba, inda yace yana fata wannan tattaunawa zata zamo ta karshe a jerin tattaunawa daban daban da suka yi da shuwagabannin kungiyar Malaman jami’a, ASUU, wanda daga nan sai janyewa.

KU KARANTA: PDP ta nemi kasashen Amurka da Birtaniya dasu dauki tsatstsauran mataki akan El-Rufai

Mataimakiyar daraktan watsa labaru ta ma’aikatar ilimin, Iliya Rhoda ce ta bayyana haka a madadin ministan kwadago, inda tace “Za ayi wannna zama ne domin kawo karshen yajin aikin da Malaman jami’a suka fada, kuma za ayi shi ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Feburairu.” Inji ta.

A ranar 5 ga watan Nuwambar shekarar 2018 ne kungiyar ASUU ta kaddamar da yajin aikin dindindin har sai gwamnati ta biya mata bukatunta, tare da cika duk wasu alkwawurran da gwamnatin ta daukan mata a baya.

Muhimmai daga cikin bukatun gwamnatin akwai batun antaya makudan kudade ga harkar ilimi a matakin jami’a da nufin inganta tsarin ilimin jami’a tare da samar da nagartattun dalibai, sai kuma batun biyansu hakkokinsu na alawus alawus.

A zaman karshe da ASUU tayi da gwamnati, dukkanin bangarorin biyu sun gamsu da cewa an shawo kan manya manyan bukatun da kungiyar ta sha bambam da ASUU, don haka ASUU ta nemi gwamnati ta bata lokaci domin ta kammala tattaunawa da sauran yayanta kafin ta yanke hukuncin janye yajin aikin.

Da wannan ake sa ran kungiyar ASUU za ta janye yajin aikinta nan bada jimawa idan har komai ya tafi kamar yadda suka tsara, wanda hakan zai baiwa dalibai damar komawa makarantu don cigaba da karatu, ita kuma gwamnatin Buhari za ta samu tagomashi, musamman yayin da zabe ke karatowa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel