INEC ta fara raba muhimman kayan aikin zabe

INEC ta fara raba muhimman kayan aikin zabe

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa (INEC) ta fara rabon gamagari da muhimman kayan aikin zabe ga jihohi.

Kwamishina hukumar sannan shugaban kwamitin wayar da kan ma su zabe, Festus Okoye, ne ya sanar da a jiya, Laraba, yayin wata tattauna wa da manema labarai a hedikwatar INEC ta kasa da ke Abuja.

A cewar sa, hakan ya nuna cewar hukumar INEC ta shirya tunkarar zabukan da za a fara cikin watannan.

"A yau, Laraba, da nake magana da ku a yanzu haka, an kai kayayyakin aikin zabe zuwa dakunan adana kaya manyan yankunan kasar nan. Wasu kayan tuni an mika su ga jihohi da ofisoshin kananan hukumomi," a cewar Okoye.

Wasu daga cikin gama garin kayan aikin zabe sun hada da akwatin kuri'u, kayan rubutu, kayan ma'aikatan wucin gadi da sauran su.

INEC ta fara raba muhimman kayan aikin zabe

Ma su aikin zabe
Source: Depositphotos

Okoye ya cigaga da cewa, "hatta injinan samar da hasken wutar lantarki da za a yi amfani da su mazabu an raba su zuwa ko ina.

"A saboda haka, mun umarci kwamishinonin mu na jihohi da su kara tsaurara matakan tsaro a ofishin kananan hukumomi, saboda wasu daga cikin su an kai ma su gama-garin kayan aikin zabe. :

"Yanzu haka kayan aikin zabe na musamman sun fara isa ofishin babban bankin kasa da ke kowacce jiha. Wadannan muhimman kayan aikin zaben sun hada da kuri'u da takardun shigar da sakamako."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel