Za mu rubanya adadin ma su cin moriyar N-power sau 3 - Osinbajo

Za mu rubanya adadin ma su cin moriyar N-power sau 3 - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce shirin nan na kirkiarar aiki da tallafa wa matasa da gwamnatin APC ta kirkira zau debi karin matasa miliyan 1.5 idan aka sake zaben jam’iyyar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

A jawabin da ya gabatar a jihohin Ondo da Ekiti, yayin gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa, Osinajo ya jaddada kudirin gwamnatin su na samar da aiyuka ga matasa da inganta sana’o’i.

Ya kara da cewa gwamnatin APC za ta cigaba da tabbatar da ganin an kashe kudin kasa domin inganta rayuwar ‘yan kasar. Kazalika ya jaddad cewar hatta makiyan shugaban shugaba Buhari sun san mutum ne mai kima da aiki da gaskiya.

Sannan ya bawa jama’a tabbacin cewar gwamnati za ta dauki Karin matasa da su ka kamala karatu miliyan 1.5 a karkashin shirin nan na N-Power da yanzu haka matasa 500,000 ke cin moriya.

Za mu rubanya adadin ma su cin moriyar N-power sau 3 - Osinbajo

Wasu ma su cin moriyar shirin N-power
Source: Depositphotos

Mutanen da su ka yi nasara su ne wadanda su ka shugaban da ya zage dantse wajen yaki da cin hanci, wannan shugaba shine shugaban kasa Muhammadu Buhari,” a cewar Osinbajo yayin gabatar da jawabi a wurin taron kamfen a jihar Ondo.

DUBA WANNAN: Hatsarin mota: Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP da matar sa sun mutu

Sannan ya cigaba da cewa, “samar da aiki ga matasa na daga cikin muhimman abubuwa uku da gwamnatin mu ta bawa muhimmanci.”

Osinbajo y ace ana samun karuwar matasa miliyan 1.7 da ke shiga neman aiki duk shekara bayan kamala bautar kasa (NYSC).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel