Hatsarin mota: Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP da matar sa sun mutu

Hatsarin mota: Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP da matar sa sun mutu

Philip Agu, mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a karamar hukumar Nsukka da ke jihar Enugu, yam utu sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi tare da matar sa.

Lamarin ya faru ne a yau, Laraba, yayin da Agu da matar sa ke hanyar su ta zuwa garin Enugu, kamar yadda majiyar mu ta shaida ma na.

Duk da ya rage saura kwanaki kadan a fara gudanar da zabukan shekarar 2019, majiyar mu ba ta sanar da mu ko Agu ya yi hatsari yayin da ya ke kan hanyar zuwa halartar taron siyasa ba ne.

A wani labarin na Legit.ng da ya shfi jam'iyyar PDP, kun ji cewar jam’iyyar ta sanar da dakatar da yakin neman zaben dan takarar ta na gwamna a jihar Zamfara biyo bayan yawaitar kai hare-hare a jihar.

Hatsarin mota: Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP da matar sa sun mutu

Tutar jam'iyyar PDP
Source: Twitter

Dan takarar gwamnan jihar Zamfara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Bello Matawalle, ne ya sanar da hakan yayin wata ganawa da manema labarai da ya yi jiya, a ranar Talata, a garin Gusau.

Ina mai bayar da sanarwar cewar na dakatar da dukkan harkokin yakin neman zabe na saboda yawaitar kai hare-hare kan al’umma da ‘yan bindiga ke yi a jihar Zamfara.

“Ina kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su bullo da hanyoyi na zahiri da za su kawo karshen aiyukan ta’addanci a jihar Zamfara,” a cewar Matawalle.

DUBA WANNAN: Rigimar duniya: Matashi ya kai karar iyayensa saboda sun haife shi babu izinin

Matawalle ya nuna damuwar sa bias yadda aiyukan ‘yan ta’adda a Zamfara ke dukan sabon salo ta yadda ‘yan ta’addar ke tantance wadanda zasu kasha ko kuma su yi garkuwa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel