Kamfe: Atiku ya gudanar da taron yakin zaben sa a jihar Borno da Yobe

Kamfe: Atiku ya gudanar da taron yakin zaben sa a jihar Borno da Yobe

A yau Laraba 6 ga watan Fabrairu, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya gudanar da taron sa na yakin neman zabe cikin jihar Borno da Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Al'ummar jihohin biyu sun fito kwansu da kwarkwata domin nun goyon baya ga tsohon mataimakin shugaban kasa tare da tawagar sa ta jiga-jigan jam'iyyar PDP kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Atiku yayin gabatar da jawabai a jihar Borno

Atiku yayin gabatar da jawabai a jihar Borno
Source: Twitter

Tururuwar al'umma yayin taron yakin zaben Atiku a jihar Borno

Atiku yayin dirar sa a jihar Yobe

Atiku yayin dirar sa a jihar Yobe
Source: Twitter

Cika da batsewar jihar Yobe yayin taron yakin zaben Atiku

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus tare da shugaban kungiyar 'yan aware na jam'iyyar APC; Buba Galadima

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus tare da shugaban kungiyar 'yan aware na jam'iyyar APC; Buba Galadima
Source: Twitter

Uche Secondus tare da jiga-jigan PDP a jihar Yobe

Uche Secondus tare da jiga-jigan PDP a jihar Yobe
Source: Twitter

Sakamakon babban zaben kujerar shugaban kasar Najeriya da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu, Atiku yayin shan alwashi na kawo karshen ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan, ya yi kira ga al'ummomin biyu da su jefa masa kuri'u.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Atiku ya girgiza magoya baya yayin yakin zabe a jihar Bauchi

Atiku ya tunatar da al'ummar jihohin biyu dangane da gazawar gwamnatin jam'iyyar APC ta fuskar rashin tsaro, tabarbarewa harkokin ilimi da lafiya gami da rashin samar da ababe na more rayuwa cikin jihohin su.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Wazirin Adamawa a jiya Talata ya jijjiga magoya bayan sa yayin taron yakin neman zabe cikin cika da tumbatsar al'umma a jihar Bauchi da kuma Taraba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel