Yaki-dan-zamba: An maida tsohon dogarin Tinubu jihar Kwara matsayin kwamishinan 'yan sanda

Yaki-dan-zamba: An maida tsohon dogarin Tinubu jihar Kwara matsayin kwamishinan 'yan sanda

Majalisar aikin yan sanda ta tabbatar da nadin sabbin kwamishanonin yan sandan Najeriya na jihohi 36 a birnin tarayya Abuja bisa ga canjin da sabn sifeto janar na hukumar yan sanda, IGP Adamu Mohammad ya bukata.

Legit.ng ta samu wannan labari ne a wata takardar manema labarai da kakakin majalisar, Ikechukwu Ani, ya saki a ranan Laraba, 6 ga watan Febrairu, 2019.

Yaki-dan-zamba: An maida tsohon dogarin Tinubu jihar Kwara matsayin kwamishinan 'yan sanda

Yaki-dan-zamba: An maida tsohon dogarin Tinubu jihar Kwara matsayin kwamishinan 'yan sanda
Source: UGC

KU KARANTA: Zakzaky ya umurci 'yan shi'a su kauracewa zaben 2019

Sai dai duk a cikin su canjin da aka samu na kwamishinan 'yan sandan jihar Kwara dake a yankin Arewa ta tsakiya shine yafi daukar hankalin musamman ma saboda irin siyasar da ake tunanin an sa wajen yin hakan.

Mun samu cewa dai sabon kwamishinan 'yan sandan da aka tura jihar ta Kwara dai a baya yayi zama babban dogarin tsohon gwamnan jihar Legas Cif Bola Tinubu tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, Egbetokun Kayode .

Sabon nadin dai yayi ta jawo cece kuce musamman ganin irin takun sakar dake tsakanin shi tsohon gwamnan jihar ta Legas, Cif Bola Tinubu da kuma tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Bukola Saraki.

A wani labarin kuma, Wata kungiya wadda ba ta gwamnati ba mai rajin kare demkradiyya data kunshi gamayyar wasu jam'iyyun siyasa a Najeriya watau Coalition of United Political Parties (CUPP) ta ce ta bankado wasu shiri da hukumar EFCC ke yi na cafke korarren alkalin alkalai, Mai shari'a Walter Onnoghen.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a ta bakin kakakin ta na kasa Mista Imo Ugochinyere wanda ya bayyanawa manema labarai hakan yayin da yake zantawa da su a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel