Abinda na fadawa sarakunan Nasarawa yayin ganawar sirri da mu kayi - Buhari

Abinda na fadawa sarakunan Nasarawa yayin ganawar sirri da mu kayi - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana abinda ya fadawa shugabanni da masu rikeda sarautun gargajiya na jihar Nasarawa a taron sirrin da ya yi da su a gidan gwamnati a lokacin da ya isa gidan gwamnati a Lafia.

Abinda na fadawa sarakunan Nasarawa a cikin sirri - Buhari

Abinda na fadawa sarakunan Nasarawa a cikin sirri - Buhari
Source: Twitter

Ya ce, "Na fada musu cewar zan cigaba da bayar da himma a kan abubuwa uku da na mayar da hankali a kai wadanda suka hada da samar da zaman lafiya, inganta tattalin arziki da yaki da rashawa.

"An inganta zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ila wasu tsirarun kananan yan mata da 'yan ta'addan ke amfani da su wurin aikata kisar bakin wake.

DUBA WANNAN: Hotunan yadda al'ummar Nasarawa suka fito tarbar Buhari

"Tattalin arzikin kasa yana cigaba duba da yadda mutane suka rungumi noma kuma mun rage rashawa."

Ya ce gwamnatinsa tana habaka layin dogo, titunan mota, wutar lantarki, samar da takin zamani ga manoma da sauransu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yabawa Gwamna Umaru Al-Makura bisa kokarinsa na samar da ayyukan more rayuwa ga al'ummarsa da inganta zaman lafiya a jihar.

Shugaba Buhari ya kuma daga hannun dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar, Injiniya Abdullahi Alhaji Sule kuma ya yi kira ga al'ummar Nasarawa su fito kwansu da kwarkwata su kada masa kuri'u.

A jawabinsa, Gwamna Al-Makura ya ce, "Shugaba Buhari ya kammala aikin gadar Oweto, ya kaddamar da shirin ciyar da daliban frimare a jihar, ya samar da karin jami'an tsaro, yana kafa transiforma mai karfin 330 KVA a Akurba, ya kuma umurci NNPC ta fara neman man fetur a jihar, ya samar da N-Power da sauransu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel