Zabe: Mutuncin Najeriya na ke karewa - El-Rufa'i ya kare katobarar da ya yi

Zabe: Mutuncin Najeriya na ke karewa - El-Rufa'i ya kare katobarar da ya yi

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi karin bayani a kan barazanar da ya yiwa 'yan kasashen waje da ke da niyyar yin katsalandan a babban zaben Najeriya da za a gudanar a cikin watan Fabrairu.

A wata hira da akayi da shi a gidan talabijin na NTA, gwamnan ya ce duk wani dan kasan waje da ke shirin yin katsalandan a zaben Najeriya zai koma kasarsa a cikin jakar gawa. Ana amfani da wannan jakar ne domin daukar gawarwaki.

Wannan furucin ya janye cece-kuce tsakanin al'umma har ta kai ga jam'iyyar PDP tayi kira ga kasashen waje su saka takunkumin hana tafiye-tafiye a kan gwamnan.

El-Rufai ya yi karin haske kan barazanar da ya yi akan wadanda ke son katsalandan a zabe

El-Rufai ya yi karin haske kan barazanar da ya yi akan wadanda ke son katsalandan a zabe
Source: Depositphotos

Sai dai wani sako da hadimin gwamnan, Samuel Aruwan ya fitar a madadin gwamnan a ranar Laraba, El-Rufai ya ce babu wani aibi ko laifi a cikin abinda ya fadi.

DUBA WANNAN: EFCC: Shaida ya bayyana yadda Shekarau da wasu mutane 2 suka kasafta N950m

Ya ce abinda ya fadi ba kalaman tayar da hankali bane illa kalma da ke kare kima da darajar Najeriya a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta ga wadanda ke kokarin yin katsalandan cikin harkokin kasar.

A cewarsa, "A yayin da gwamna El-Rufai ya yi magana a shirin Tuesday Night Live na NTA, ya fadi kalamai ne da duk dan kasa mai kishin Najeriya zai fahimta. Ya kare kima ne da darajar Najeriya a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta daga wadanda ke kokarin mayar da ita wata alkarya domin kwadayin mulki," inji sanarwar.

"Rashin yin katsalandan a zaben wata kasa doka ce cikin dokokin kasa da kasa. Yin barazanar katsalandan a zaben wata kasa na nufin yaki ne. Ya kamata a gargadi wadanda ke niyyar cin zabe ta hanyar neman taimakon kasashen waje. Yan kasa ne kawai ke da ikon canja gwamnati.

"Mallam Nasir El-Rufai ya yi kira ne a sanya idanu a kan abinda ke faruwa ya kuma gargadi kasashen waje a kan yiwa Najeriya katsalandan.

"El-Rufai mutum ne da ya baya goyon bayan masu neman raba kan 'yan Najeriya ta hanyar amfani da kabila ko addini. Baya goyon bayan tashin hankali, abinda ya sa a gaba shine zaman lafiya.

"Ya kamata masu yadda karerayi su dena," inji El-Rufai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel