Masu so Birtaniya ta fita daga EU 'yan wuta ne - Donald Tusk

Masu so Birtaniya ta fita daga EU 'yan wuta ne - Donald Tusk

- Shugaban kungiyar Tarrayar Turai Donald Tusk ya bayyana wadanda ke neman kasar Birtaniya ta fita daga Tarrayar Turai ba tare da wani kyakkyawan shiri ba a matsayin ‘yan wuta

- Ya ce Tarrayar Turai za ta matsa lamba a kan yarjejeniyar barin iyakar kasar Ireland a bude ko da kuwa akwai batun ficewar Birtaniya domin wanzar da zaman lafiya

- Amma Mista Tusk da kuma Mista Varadkhar suna da shirin ko ta kwana a kan batun ficewar Birtaniya daga Tarrayar Turai

Shugaban kungiyar Tarrayar Turai Donald Tusk ya bayyana wadanda ke neman kasar Birtaniya ta fita daga Tarrayar Turai ba tare da wani kyakkyawan shiri ba a matsayin ‘yan wuta.

Ya bayyana haka ne bayan zantawarsu su da Ministan Ireland Leo Varadkar a Brussels.

Ya ce Tarrayar Turai za ta matsa lamba a kan yarjejeniyar barin iyakar kasar Ireland a bude ko da kuwa akwai batun ficewar Birtaniya domin wanzar da zaman lafiya.

Amma Mista Tusk da kuma Mista Varadkhar suna da shirin ko ta kwana a kan batun ficewar Birtaniya daga Tarrayar Turai.

Masu so Birtaniya ta fita daga EU 'yan wuta ne - Donald Tusk

Masu so Birtaniya ta fita daga EU 'yan wuta ne - Donald Tusk
Source: UGC

'Yan majalisar dokoki a Birtaniya kamar irin su Andrea Leadsom tuni suka fara mayar da martani a kan irin wadannan kalamai na Mista Tusk.

Misis Leadsom, wadda tana daya daga cikin wadanda suka yi ta kiraye-kirayen ficewar Birtaniyan, ta bayyana kalaman nasa a matsayin ''kalaman da na sani'' kuma ''kalaman da ba za su taimaka ba.''

KU KARANTA KUMA: Buhari na kewaye da miyagun mutane – Inji Shehu Sani

'Yar majalisar, wadda kuma 'yar jami'iyyar Conservative ce ta bayyana cewa ''ba shi da da'a.''

A wani lamari na daban, babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, jam’iyyar PDP ta yi kira da babban murya ga kasashen duniya dasu hanzarta janye alfarmar tafiye tafiye da gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai ke da shi sakamakon kalaman batanci daya furta akansu.

Kakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbodiyan ne ya sanar da haka a ranar Laraba, 6 ga watan Feburairu yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yace PDP na kira ga kasashen Duniya dasu haramta ma El-Rufai tafiye tafiye saboda kalaman daya furta da ka iya tunzura jama’a su kawo cikas ga zaben 2019.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel