Najeriya za ta ruguje idan aka zabi Buhari - Peter Obi

Najeriya za ta ruguje idan aka zabi Buhari - Peter Obi

Peter Obi, dan takaran kujeran mataimakin shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), yace idan aka kuskura aka zabi shugaba Muhammadu Buhari, Najeriya za ta ruguje.

Jaridar PUNCH ta hakaito wannan jawabi ne yayinda yake magana da manema labarai a kan titin Awka, babban birnin jihar Anambara.

Yace gwamnatin All Progressives Congress (APC) ba tada karfin mulki saboda haka jama'a su kawar da wannan gwamnati a zabe mai zuwa.

Najeriya za ta ruguje idan aka zabi Buhari - Peter Obi

Najeriya za ta ruguje idan aka zabi Buhari - Peter Obi
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta cika hannu da yan damfarar yanar gizo 11

Yace: "Muna kamfen kan titi domin aika saknmu ga yan Najeriya. Muna fada musu cewa wannan zaben na rana goben yaranmu ne."

"Muna samun karfin gwiwa da irin goyon bayan da muke samu a ko ina, ba a kudu maso gabas kadai ba saboda mutane sun ga gaskiyan al'amari."

"Sun gani cewa wannan gwamnati ba tada karfi da salon mulkin Najeriya."

"Sun gano cewa idan aka kuskura aka bari Buhari ya cigaba kasar nan za ta ruguje. Tun da mun kawo kasar na rugujewa, wajibi ne kowa ya mara mana baya."

"Mun ga yadda rashin tsaro ke kara yawa kulli yaumin. Mun tashi daga na bakwai zuwa na uku cikin kasashe marasa zaman lafiya bayan kasar Afghanistan da Iraqi. Wannan abin damuwa ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel