Yadda maganin sauro ya hallaka 'yan gida daya su 3 a Kano

Yadda maganin sauro ya hallaka 'yan gida daya su 3 a Kano

Labarin da ke zuwa mana ya nuna cewa wasu yan mata uku da suka fito daga gida daya sun rasa ransu sanadiyar maganin sauro a jihar Kano.

Yaran masu suna, Zakiyya mai shekara 17, Walida mai shekara 16, da kuma Wasila mai shekara 11 sun kwanta ne a cikin dakin da suka fesa maganin sauro sannan kuma suka toshe ko'ina.

Zuwan mahaifinsu ke da wuya don ya tashe su don su yi shirin tafiya makaranta da safe, sai kawai ya tarar da gawarwakinsu.

Yadda maganin sauro ya hallaka 'yan gida daya su 3 a Kano

Yadda maganin sauro ya hallaka 'yan gida daya su 3 a Kano
Source: Depositphotos

Mai taimaka wa gwamnan Kano kan harkokin matasa Habeeb Ahmad ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce 'yan matan sun rasu ne a ranar Lahadi.

Habib Ahmad ya musanta cewa guba ce ta halaka 'yan matan.

"Mun kai su asibiti kuma likita ya tabbatar mana da cewa maganin sauro ne da suka yi amfani da shi ya haddasa rasuwarsu".

KU KARANTA KUMA: Buhari na kewaye da miyagun mutane – Inji Shehu Sani

Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar al'amarin, kuma ta ce maganin sauro ne silar rasuwar tasu.

Abdullahi Haruna na rundunar ya ce "gaskiya ne likitoci sun ce maganin sauro ne, amma za mu ci gaba bincike kuma za mu sanar da ku idan mun kammala".

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel