Magoya bayan APC a Bauchi sun sauya sheka zuwa PDP, sun yi bikin kona tsintsiya

Magoya bayan APC a Bauchi sun sauya sheka zuwa PDP, sun yi bikin kona tsintsiya

- Kimanin magoya bayan APC da sauran jam'iyyun siyasa 10,000 ne suka sauya sheka a jihar Bauchi

- Masu sauya shekar sun kona tsintsiya a bainar jama'a, sun ce basu amfana da komai ba a jam'iyyar

- An ba masu sauya shekar tabbacin shiga a dama dasu a harkokin PDP

Akalla magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da wasu jam’iyyun siyasa 10,000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Bauchi a ranar Talata, 5 ga watan Fabrairu inda hakan ya ba babbar jam’iyyar adawar karin karfi.

Masu sauya shekar sun samu jagorancin tsohon mataimakin gwamna, Sagir Aminu Saleh a lokacin gangamin kamfen din dan takarar Shugaban kasa na PDP a babban filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa.

Magoya bayan APC a Bauchi sun sauya sheka zuwa PDP, sun yi bikin kona tsintsiya

Magoya bayan APC a Bauchi sun sauya sheka zuwa PDP, sun yi bikin kona tsintsiya
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa masu sauya shekar, yayinda suke sanar da sauya shekar nasu sun bayyana cewa a lokacin da suke jam’iyya mai mulki basu amfana da komai ba saima bata lokacinsu da dukiyoyinsu. Sun kuma yi bikin kona tsintsiya wanda alama ce ta APC.

Masu sauya shekar sun samu tarba daga Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na Gombe, wanda shine daraktan kamfen din jam’iyyar na yankin.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin sama ta samu karin jiragen yaki 22 domin yakar Boko Haram da sauransu

Gwamnan ya basu tabbacin samun muhimman mukamai a jam’iyyar idan tayi nasarar lashe zabe mai zuwa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel