Hotuna: Hukumar EFCC ta cika hannu da yan damfarar yanar gizo 11

Hotuna: Hukumar EFCC ta cika hannu da yan damfarar yanar gizo 11

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta damke wasu matasa masu damfarar jama'a ta yanar gizo a garin Ilori, babbar birnin jihar Kwara.

Majiyar Legit ta samu wannan labari ne a wata jawabi da hukumar ta saki a ranan Laraba, 6 ga watan Febrairu, 2019.

Jawabin tace: Jami'an hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC shiyar Ilori ta damke madamfara 11 bisa ga cinne da akayi a Agric Estate. Ilori, jihar Kwara.

Matasan wadanda aka damke ranan 4 ga watan Febrairu, 2019 misalin karfe 11 na dare sune Oluyomi Kadri, Adeseye Ogundele, Olasoji Alabi, Abdullahi Saliu, Abdullahi Ibrahim da Abolarin Kayode.

Hotuna: Hukumar EFCC ta cika hannu da yan damfarar yanar gizo 11

Hotuna: Hukumar EFCC ta cika hannu da yan damfarar yanar gizo 11
Source: Facebook

A cikinsu akwai mata biyar; Momoh Aminat, Momoh Nimota, Kelvin Blessing, Sunday Ruth and Oyinlola Awokunle.

Hotuna: Hukumar EFCC ta cika hannu da yan damfarar yanar gizo 11

Hotuna: Hukumar EFCC ta cika hannu da yan damfarar yanar gizo 11
Source: Facebook

Daga cikin abubuwan da aka samu a hannayensu takardun filaye, manya motoci uku, kwamfyutoci, yanar gizo, wayoyi, da katin banki.

Wasu daga cikinsu sun amince da zargin da ake tuhumarsu da shi na damfarar mutane a yanar gizo kuma za'a gurfanar da su a kotu muddin aka kammala bincike akansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel