Zabe: Gwamnatin Kano ta amince da bawa Atiku filin yin taro

Zabe: Gwamnatin Kano ta amince da bawa Atiku filin yin taro

- Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bayar da umurnin dakatar da gyaran Sani Abacha Stadium

- Gwamnan ya bayar da wannan umurnin ne domin bawa dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar damar kaddamar da yakin neman zabensa a filin

- A baya, jam'iyyar ta PDP ta zargi gwamnatin jihar Kano da kirkiro gyran ne kawai domin hana su amfani da filin wasannin

Daga karshe: Gwamnatin Kano ta bawa PDP izinin amfani da filin wasa domin kamfen

Daga karshe: Gwamnatin Kano ta bawa PDP izinin amfani da filin wasa domin kamfen
Source: Depositphotos

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya umurci dan kwangilar da kula da gyaran filin wasanni na Sani Abacha da ke Kano ya dakata domin bawa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar damar kaddamar da yakin neman zabensa.

Gwamnan ya sanar da hakan ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba a ranar Laraba.

DUBA WANNAN: Jigo a APC ya ce kowa ya zabi abinda ya ke so bayan zaben Buhari

Ya ce, "dakatar da gyarar ba ta shafi garambawul da ake yiwa dakkunan wasanni na cikin gida ba"

Kazalika, an umurci dan takarar ya kwashe dukkan kayayakin gyara da motoccinsa har zuwa lokacin da za a kammala yakin neman zaben na Atiku Abubakar.

Har ila yau, an umurci kungiyar kwallon kafa na jihar, wato Kano pillars su rika amfani da filin wasa na Sabon Gari domin atisayensu.

A baya, shugaban riko na jam'iyyar PDP reshen jihar Kano, Rabiu Bichi ya zargi gwamnatin jihar Kano ta kirkirar gyaran dakin filin wasannin domin hana jam'iyyar PDP samun daman amfani da filin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel