Cikin Hotuna: Atiku ya girgiza magoya baya yayin yakin zabe a jihar Bauchi

Cikin Hotuna: Atiku ya girgiza magoya baya yayin yakin zabe a jihar Bauchi

A jiya Talata 5 ga watan Fabrairu, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya dira cikin Bauchin Yakubu domin girgiza da aringizon magoya baya yayin gudanar da taraon sa na yakin neman zabe.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon mataimakin shugaban kasar ya gudanar da taron sa na yakin neman a jihar Bauchi yayin ci gaba da shawagi da kuma karade jihohi 36 na Najeriya wajen neman magoya baya.

Yayin ci gaba da gabatowar babban zaben kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu, Atiku bayan ziyartar jihar Taraba a jiya ya kuma fantsama jihar Bauchi domin taron sa na yakin neman zaben cikin wani sabon salo tare da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

Atiku yayin dirar sa a jihar Bauchi

Atiku yayin dirar sa a jihar Bauchi
Source: Twitter

Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara tare da gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo yayin tarbar Atiku a filin jirgin sa na Abubakar Tafawa Balewa

Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara tare da gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo yayin tarbar Atiku a filin jirgin sa na Abubakar Tafawa Balewa
Source: Twitter

Atiku yayin fasa taro a jihar Bauchi

Atiku yayin fasa taro a jihar Bauchi
Source: Twitter

Al'ummar yayin tururuwa a taron yakin zaben Atiku a jihar Bauchi

Al'ummar yayin tururuwa a taron yakin zaben Atiku a jihar Bauchi
Source: Twitter

Kakakin majalisar wakilai yayin fasa taro a yakin neman zaben Atiku cikin jihar Bauchi

Kakakin majalisar wakilai yayin fasa taro a yakin neman zaben Atiku cikin jihar Bauchi
Source: Twitter

Atiku da jiga-jigan PDP yayin girgiza magoya baya a taron yakin zabe cikin jihar Bauchi

Shugaban PDP na kasa, Uche Secondus, Atiku, Dankwambo da Sanata Bala Muhammad

Shugaban PDP na kasa, Uche Secondus, Atiku, Dankwambo da Sanata Bala Muhammad
Source: Twitter

Baya ga Honarabul Dogara, Atiku ya gudanar da taron sa na yakin zabe kafada-da-kafada da dan takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi na jam'iyyar PDP, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, wanda ya kasance tsohon Ministan birnin tarayya.

Rahotanni sun bayyana cewa, jihar Bauchi da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ta cika ta batse da dumbin al'umma magoya baya da suka kwankwadi akida tare busa sarewa mai amsa amo na goyon bayan Atiku da jam'iyyar sa ta PDP.

KARANTA KUMA: Addu'ar Fasto Adeboye ta yi tasiri yayin kifewar jirgin Mataimakin shugaban kasa

Cikin zayyana jawaban sa, Atiku ya sha alwashi kawo karshen fatara gami da talauci da ta yiwa al'ummar kasar nan katutu ta hanyar shimfida kyawawan tsare-tsare ma su tasirin gaske wajen habaka tattalin arzikin kasar nan.

Kazalika jagoran kungiyar yakin neman zaben Atiku na reshen Arewa maso Gabas, Alhaji Ibrahim Dankwambo, yayin halartar taron ya kuma yi kira ga al'umma wajen jefa kuri'un su ga Atiku yayin babban zaben da ba bu shakka zai fidda kasar nan zuwa tudun tsira.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel