Buhari na kewaye da miyagun mutane – Inji Shehu Sani

Buhari na kewaye da miyagun mutane – Inji Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari na kewaye da miyagun mutane

- Sani ya yi zargin cewa wadanda suka yi aiki tare da tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar wajen siyar da kadarorin kasar sune suke aiki tare da Buhari

Sanata Shehu Sani a ranar Laraba, 6 ga watan Fabrairu yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari na kewaye da miyagun mutane wadanda suka yi aiki domin sama wa tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo zango na uku.

Sani, wanda ya kasance sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya yi ikirarin ne yayinda yake martani ga furucin shugaba Buhari wanda yayi hannunka mai sanda ga tsohon Shugaban kasa Obasanjo.

Buhari na kewaye da miyagun mutane – Inji Shehu Sani

Buhari na kewaye da miyagun mutane – Inji Shehu Sani
Source: UGC

A wani rubutu da ya wallafa a shafin twitter a ranar 6 ga watan Fabrairu, dan majalisan ya kuma bayyana cewa wadanda suka yi aiki tare da tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar wajen siyar da kadarorin kasar sune suke aiki tare da Buhari.

Kafin zaben 2015 wanda ya kawo Buhari kan mulki, Shugaban kasar ya kaddamar da cewa zai yi takara ne na zango guda kacal sannan cewa ba zai sake neman tazarce ba.

Buhari a daya daga cikin gangamin kamfen dinsa da ya gudana a jihar Ondo a ranar 5 ga watan Fabrairu sai yayi wani hannunka mai sanda ga Obasanjo kan kokarin da yayi na barazana ga damokradiyar kasar na neman zama kan mulki fiye da zango na biyu.

KU KARANTA KUMA: Ga jerin abubuwan da Atiku ya fi sha’awa a rayuwarsa

“Yanzu muke kammala zango na daya sannan muna neman na biyu. Bayan wannan , kundin tsarin mulki bata bamu damar kara wani ba. Akwai wasu da suka yi kokarin neman kari amma basu yi nasara ba. Ya kamata mu koyi darasi daga kurakurensu,” inji Buhari a Akure.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel