PDP ta nemi kasashen Amurka da Birtaniya dasu dauki tsatstsauran mataki akan El-Rufai

PDP ta nemi kasashen Amurka da Birtaniya dasu dauki tsatstsauran mataki akan El-Rufai

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, jam’iyyar PDP ta yi kira da babban murya ga kasashen duniya dasu hanzarta janye alfarmar tafiye tafiye da gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai ke da shi sakamakon kalaman batanci daya furta akansu.

Kaakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbodiyan ne ya sanar da haka a ranar Laraba, 6 ga watan Feburairu yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yace PDP na kira ga kasashen Duniya dasu haramta ma El-Rufai tafiye tafiye saboda kalaman daya furta da ka iya tunzura jama’a su kawo cikas ga zaben 2019.

KU KARANTA: Zamu halaka duk wanda yayi mana katsalandan a zabe – El-Rufai ga yan kasashen waje

Legit.ng ta ruwaito gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya yi barazanar halaka duk wani dan kasar waje da yayi ma Najeriya katsalandan a yayin babban zaben 2019 dake karatowa, wanda zai gudana a watan Feburairu da watan Maris.

“Duk masu kira ga kasashen waje dasu shigo su yi mana katsalandan, toh muna jiran mu ga wanda zai mana katsalandan, sai mun mayar dasu a cikin jakkunan gawa.” Inji Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai.

Sai dai cikin martanin da PDP ta mayar ta ce: “Har yanzu yan Najeriya suna cikin dimuwa da kalaman El-Rufai, wanda ya furta a gidan talabijin na kasa cewa zasu mayar da yan kasashen waje masu sa ido don tabbatar da an yi zaben gaskiya a Najeriya, zuwa kasashen a cikin jakkunan ajiyan gawa.

“Wannan barazana da me yayi kama? Don haka muke kira ga kwamitin zaman lafiya ta kasa da ta gaggauta gayyatar El-Rufai ya gurfana gabanta, musamman duba da nauyin kalaman daya furta wanda barazana ne ga gudanar da zaben gaskiya da gaskiya.” Inji shi.

Daga karshe PDP tace duba da maganganun da El-Ruafi, wanda Buhari yayi da kuma wanda APC tayi, zata janye daga yarjejeniyar zaman lafiya da ta rattafa hannu akansa tsakaninta da cibiyar zaman lafiya ta kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel