An yanke wa shugaban kungiyar direbobi hukuncin rataya, shekaru takwas bayan ya kashe dansanda

An yanke wa shugaban kungiyar direbobi hukuncin rataya, shekaru takwas bayan ya kashe dansanda

- Tun a 2011 yayi kisan a jihar Legas

- Dansanda ne ya kashe dan shekara 32

- Kotu tace a rataye shi ba sassauci

An yanke wa shugaban kungiyar direbobi hukuncin rataya, shekaru takwas bayan ya kashe dansanda

An yanke wa shugaban kungiyar direbobi hukuncin rataya, shekaru takwas bayan ya kashe dansanda
Source: UGC

A jiya laraba ne, kotun Tarayya dake Ikeja a birnin Legas, ta yanke wa Saheed Arogundade, tsohon Chairman na National Union of Road Transport Workers (watau NURTW), ta Boudary/Aiyetoro Unit, dake jihar Lagos hukuncin rataya.

Matashin, ya kashe matashin dansanda Gbenga Oladipupo ne a 2011 a jihar Legas, bayan taqaddama da ta hado su, dansandan ya rasu yana da shekaru 32.

Justice Olabisi Akinlade ce tayi hukuncin, ta kuma wanke tare da sakin Mustapha Layeni, Adebayo Abdullahi, Seyi Pabiekun, Sikiru Rufai da Yusuf Arogundade, wadanda ake zargi da hada baki suyi kisan.

GA WANNAN: Karin hasken da soji suka bayar kan rahotannin mamaye garuruwan Adamawa

Kafin dai tayi hukuncin, saboda wanda ake zargin yana da 'yan daba magoya baya, sai da Alkaliyar tasa aka rufe kotun da mukullai aka bata mabudan ta ajje a wurinta.

A hukuncinta, tace, "kotu ta tabbatar kai Saheed Arogundade kayi niyya kuma ka kashe Gbenga Oladipupo, don haka kaima za'a rataye ka har sai ka mutu. Allah yaji qanka"

Da jin haka dai, mai laifin ya fadi warwas a kasa, su kuwa danginsa suka yi ta rusa kuka.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel