EFCC na neman kotu ta bata wata dama kan tsohon shugaban NIA, ga damar

EFCC na neman kotu ta bata wata dama kan tsohon shugaban NIA, ga damar

- $43,449,947,000 aka kama wurin matarsa

- Oke da matarsa basu bayyana a kotu yau ba

- Ya shugabanci NIA, hukumar leken asiri ta Najeriya

EFCC na neman kotu ta bata wata dama kan tsohon shugaban NIA, ga damar

EFCC na neman kotu ta bata wata dama kan tsohon shugaban NIA, ga damar
Source: Instagram

Hukumar hana ta'annati kan kudaden Najeriya, EFCC, tace tana bukatar kotu ta bata waranti, watau sammacin halartar kararsu a kotu, kan Mista Oke da matarsa wadanda aka kama da $43,449,947, 000 a Legas shekaru biyu da suka wuce.

An kama kudin ne a Flat 7B, No 16 Osborne Road, Osborne Towers, Ikoyi a Lagos, bayan da wani mai gadi yaga Madam Oke tana hawa saman gini niqi-niqi da jakunkuna kamar ta dauko kayan gwanjo, inda ya je ya gaya wa gwamnati.

GA WANNAN: Yadda duniya tayi asarar $200m, bayan mai gadinsu ya mutu bai fadi lambar sirrin ba

Tuni dai aka baiwa mai tonon sililin miliyoyin nairori, ladan tonen nasa, aka kuma kori Mista Oke daga shugabanci NIA din, hukumar leken asirin muggai masu neman Najeriya da sharri a ciki da wajen Najeriya.

Alkali Justice Chukwujekwu Aneke, yace zai bada sammacin in aka rubuto kuma aka kawo masa fayil din kes din a hannunsa, a gobe 7-02-2019, amma ba a baka ba kamar yadda EFCC din tayi, bayan da ta kasa kawo wanda ake zargin da matarsa gaban kotu.

Duk shekarun nan dai, sai yanzu ne aka kai wannan tahaliki kotu, tare da tsohon SFG, Babachir Lawal, shima kan zargi na handama a 2016, bayan an sauke shi daga mukaminsa, lamari da wasu ke gani ko dai don zabe yazo ne ko kuma akwai lauje cikin nadi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel