Masu sanya ido kan zabukan Najeriya na tarayyar Turai sun maida martani kan kalaman Malam Nasir Elrufai

Masu sanya ido kan zabukan Najeriya na tarayyar Turai sun maida martani kan kalaman Malam Nasir Elrufai

- EU ta maida martani bisa furucin da gwamnan jihar Kaduna yayi

- Wannan furuci bazai hana mu yin duba a bisa sha'anin zabe ba cewar EU

- Hukumar zabe ta INEC ce ta nemi gudummawa da EU dan taimaka mata wajen zabe

Masu sanya ido kan zabukan Najeriya na tarayyar Turai sun maida martani kan kalaman Malam Nasir Elrufai

Masu sanya ido kan zabukan Najeriya na tarayyar Turai sun maida martani kan kalaman Malam Nasir Elrufai
Source: UGC

Kungiyar sanya ido akan sha'anin zabe a Najeriya ta Tarayyar Turai watau EU ta maida martani bisa furucin da gwamnan jihar Kaduna Mal.Nasir El-rufai yayi.

Gwamnan yace sojojin Najeriya zasu kashe duk wani sojan katsalandan da yayi magagin shigo wa Najeriya wanda ba dan kasar ba kan sha'anin zabe.

EU tace wannan batu bazai sanya ta janyewa ba wajen sanya ido akan zaben da zai gudana a ranar 16 ga watan Fabrairun ba.

GA WANNAN: Jam'iyyar AA ta Rochas a Imo, ta fara aikin ganin shugaba Buhari ya zarce a wannan watan

Kungiyar ta kara da cewa zasu cigaba da gudanar da shirye shiryen su akan sha'anin tsaro daga yanzu har zuwa bayan zabe.

"EU tana shiga harkar zaben kasar ne biyo bayan neman ta da hukumar kasar keyi wanda hakan ya soma ne tun daga shekara ta 1999,wannan shine karo na Shida da EU ke sanya ido akan sha'anin zaben Najeriya."

Hukumar zabe ta kasa INEC ce ta gayyaci EU dan taimaka mata wajen gudanar da zaben shekara ta 2019.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel