Gobara ta lakume wani dan jariri mai watanni 3 a Duniya kacal a Kano

Gobara ta lakume wani dan jariri mai watanni 3 a Duniya kacal a Kano

Hukumar kashe gobara ta jahar Kano ta sanar da mutuwar wani dan karamin yaro, jariri mai watanni uku kacal da haihuwa, a unguwar Sheka Yankaji cikin karamar hukumar Kumbotso ta jahar Kano, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin hukumar, Alhaji Saidu Mohammed ne ya bayyana haka a yayin zantawa da manema labaru a ranar Laraba, 6 ga watan Feburairu a garin Kano, inda yace an gano barbashin gawar jaririn ne bayan wutar ta cinye.

KU KARANTA: Yadda masoya suka yi dafifi a yayin yakin neman zaben Buhari a Benuwe

Kaakaki Saidu yace wani gida mai dakuna biyu ne ya kama da wuta, amma sai bayan an jami’an kwana kwana sun kashe wutar ne aka gano gawar yaron a karkashin baraguzan ginan da suka sha wuta suka fadi.

“Da misalin karfe 1 na daren Laraba ne wata Hajiya Laraba Usman ta kiramu tana shaida mana tashin wutar gobara a wani gida dake unguwar Shekan Yankaji , a karamar hukumar Kumbotso, nan da nan muka aika da jami’anmu zuwa gidan inda suka kashe wutar.

“Sai dai ko da muka isa gidan mun tarar da ya cinye dakunan gidan mai dakuna biyu, sa’annan a cikin baraguzan ginin muka gano gawar jariri mai watanni uku a duniya, wanda iyayensa suka barshi a cikin daki yayin da suka fita neman agaji daga wajen jama’a.” Inji shi.

Kaakaki Saidu yace tuni suka mika gawar jaririn ga mahaifinsa, Malam Mohammed Abubakar, sa’annan yayi kira jama’a dasu kasance masu taka tsantsan wajen amfani da abubuwan da ka iya sabbaba gobara, kamarsu murhun gas domin kauce ma aukuwar gobara.

A wani labarin kuma, wani karamin yaro mai shekaru bakwai, Kalid Bello ya gamu da ajalinsa a ranar juma’ar da ta gabata a cikin wata rijiya dake unguwar Ja’en Yamma, a Unguwar Sharada cikin birnin Kano.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel