Yadda karamin yaro dan shekara 7 ya gamu da ajalinsa a cikin rijiya a Kano

Yadda karamin yaro dan shekara 7 ya gamu da ajalinsa a cikin rijiya a Kano

Wani karamin yaro mai shekaru bakwai, Kalid Bello ya gamu da ajalinsa a ranar juma’ar da ta gabata a cikin wata rijiya dake unguwar Ja’en Yamma, a Unguwar Sharada cikin birnin Kano, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin hukumar kashe gobara ta jahar Kano, Alhaji Saidu Mohammed ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 6 ga watan Feburairu yayin da yake zantawa da manema labaru a jahar Kano inda yace lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:25 na safe.

KU KARANTA: Yadda masoya suka yi dafifi a yayin yakin neman zaben Buhari a Benuwe

“Wani matashi mai suna Kabiru Yahaya ne ya kira hukumarmu ta wayar tarho, inda ya shaida mana cewa wani karamin yaro ta fada cikin rijiya, cikin mintuna goma jami’anmu suka isa gidan da rijiyar take, sai dai ko kafin isarsu yaron ya rigamu gidan gaskiya

“Sai dai gawarsa kawai muka samu daman cirowa daga cikin rijiyar, sa’annan muka mika gawar ga dakacin Ja’en Yamma, Alhaji Yau Wakili, sai dai babu wani tabbaci game da abinda ya sabbaba shigan yaron cikin rijiyar, amma bincike ya kankama domin gano gaskiyan.” Inji shi.

Daga karshe kaakaki Saidu ya yi kira ga iyaye dasu dinga kula tare da sa ido akan yayansu, domin gudun kasancewarsu a gefen rijiyan gidajensu ko kuma na makwabta, ta haka ne za’a shawon kan matsalar fadawar kananan yara cikin rijiya.

A wani labarin kuma Hukumar kashe gobara ta jahar Kano ta sanar da mutuwar wani dan karamin yaro, jariri mai watanni uku kacal da haihuwa, a unguwar Sheka Yankaji cikin karamar hukumar Kumbotso ta jahar Kano.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel