Addu'ar Fasto Adeboye ta yi tasiri yayin kifewar jirgin Mataimakin shugaban kasa

Addu'ar Fasto Adeboye ta yi tasiri yayin kifewar jirgin Mataimakin shugaban kasa

A jiya Talata tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi karin haske dangane da dalilai da suka sanya ya tsira yayin kifewar jirgin sa mai saukar Angulu cikin garin Kaaba na jihar Kogi a karshen makon da ya gabata.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasar Najeriya ya tsallake rijiya da baya a karshen makon da ya gabata sakamakon hatsari na kifewar jirgin sa mai saukar Angulu yayin da ya nufaci gudanar da wani taron yakin zabe a jihar Kogi.

A yayin da ba bu ko kwarzane guda da ya samu, mataimakin shugaban kasar ya ce, ya samu tsira ta kariya daga Mahaliccin sa domin ci gaba da yiwa al'ummar Najeriya hidima wajen sauke nauyin da rataya a wuyan sa.

Addu'ar Fasto Adeboye ta yi tasiri yayin kifewar jirgin Mataimakin shugaban kasa

Addu'ar Fasto Adeboye ta yi tasiri yayin kifewar jirgin Mataimakin shugaban kasa
Source: UGC

Da ya ke gabatar da jawabai yayin taron yakin neman zabe na jam'iyyar APC da aka gudanar a babban birnin jihar Ekiti, Osinbajo ya bayyana hakan da cewar ya samu kariyar Ubangiji domin ci gaba da jajircewa wajen yiwa al'ummar Najeriya aiki tukuru.

Tsohon lauyan kolu na jihar Legas ya ce kariya ta Ubangiji ta bayu ne sakamakon yadda Fasto Enoch Adeboye, wani babban malami da ya kwarara masa addu'o'i na neman tsariya da kariyar duk wani sharri da abin ki.

Osinbajo ya ce ko shakka ba bu addu'ar Fasto Adeboye ta yi tasirin gaske sakamakon yadda karamar sa ta hango ibtila'in da zai faru a kansa kuma ya yi gaggawar tarbar ta da riga kafi wadda masu iya magana suka ce tafi magani.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Atiku ya gudanar da taron yakin neman zabe a jihar Taraba

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, mataimakin shugaban kasar ya yi furucin yadda addu'ar Fasto Adeboye ta yi tasari wajen samun tsira yayin halartar wata huduba yayin zaman coci da aka gudanar cikin birnin Lokoja na jihar Kogi.

Mataimakin shugaban kasar ya ce, karamar Fasto Adeboye ta sanya ya leka kuma ya hango mummunar barazanar da za ya fuskanta da ta sanya ya shimfida masa hannayen sa masu tabarraki wajen kwarara addu'o'i na neman tsari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran jiga-jigai na kasar nan sun jajantawa mataimakin shugaban kasar sakamakon wannan mummunan tsautsayi da ya auku a kansa tare da bayyana farin cikin su dangane da yadda ya kwashe lafiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel