Kisan ‘yar uwar Sanata: PDP ta dakatar da yakin neman zabe

Kisan ‘yar uwar Sanata: PDP ta dakatar da yakin neman zabe

Jam’iyyar PDP ta sanar da dakatar da yakin neman zaben dan takarar ta na gwamna a jihar Zamfara biyo bayan yawaitar kai hare-hare a jihar.

Dan takarar gwamnan jihar Zamfara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Bello Matawalle, ne ya sanar da hakan yayin wata ganawa da manema labarai da ya yi jiya, a ranar Talata, a garin Gusau.

Kisan ‘yar uwar Sanata: PDP ta dakatar da yakin neman zabe

Kisan ‘yar uwar Sanata: PDP ta dakatar da yakin neman zabe
Source: Depositphotos

“Ina mai bayar da sanarwar cewar na dakatar da dukkan harkokin yakin neman zabe na saboda yawaitar kai hare-hare kan al’umma da ‘yan bindiga ke yi a jihar Zamfara.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya na kokarin gurgunta gonar Onnoghen - CUPP

“Ina kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su bullo da hanyoyi na zahiri da za su kawo karshen aiyukan ta’addanci a jihar Zamfara,” a cewar Matawalle.

Matawalle ya nuna damuwar sa bias yadda aiyukan ‘yan ta’adda a Zamfara ke dukan sabon salo ta yadda ‘yan ta’addar ke tantance wadanda zasu kasha ko kuma su yi garkuwa da su.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa 'yan bindiga da suka kai farmaki a wasu garuruwa na jihar Zamfara sun nemi a biya su Naira Milyan 30 a matsayin kudin fansa kafin su saki Alhaji Ibrahim, mijin marigayiya Ade Marafa.

Ade Marafa yaya ce ga Sanata Kabiru Marafa mai wakiltan Zamfara ta Tsakiya wadda 'yan bindiga suka kashe ta.

'Yan bindigan sun kuma kone garin Ruwa Bore da ke karamar hukumar Gusau kurmus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel