Da duminsa: Ba zan canja ba idan na yi tazarce - Buhari

Da duminsa: Ba zan canja ba idan na yi tazarce - Buhari

- Shugaban kasa Buhari ya ba yan Najeriya tabbacin cewa ba zai sauya tsarinsa ba idan har suka sake zabarsa a karo na biyu

- Hakan ya biyo bayan jita-jitan cewa Shugaban kasar zai sauya sannan ya daina yiwa jama’a aiki idan aka sake zabarsa a karo na biyu

- Shugaban kasar yayi alkawarin cewa zai ci gaba da jajircewa da mayar da hankali ga aikinsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 6 ga watan Fabrairu ya ba yan Najeriya tabbacin cewa ba zai sauya tsarinsa ba idan har suka sake zabarsa a karo na biyu.

Ana ta rade-radin cewa Shugaban kasar zai sauya sannan ya daina yiwa jama’a aiki idan aka sake zabarsa a karo na biyu.

Da duminsa: Ba zan canja ba idan na yi tazarce - Buhari

Da duminsa: Ba zan canja ba idan na yi tazarce - Buhari
Source: UGC

Amma shugaba Buhari ya bayar da tabbacin cewa ba zai sauya ba a lokacin kamfen dinsa a flin wasa na Aper Aku da ke Makurdi, jihar Benue.

Shugaban kasar yayi alkawarin cewa zai ci gaba da jajircewa da mayar da hankali ga aikinsa.

Ya kuma bayyana jerin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a shekaru uku da rabi.

KU KARANTA KUMA: Ga jerin abubuwan da Atiku ya fi sha’awa a rayuwarsa

Da farko Legit.ng ya rahoto cewa dubun dubatan al’ummar jahar Benuwe da suka hada da magoya bayan jam’iyyar APC, da kuma masoya shugaban kasa Muhammadu Buhari ne suka tarbi shugaban a yayin gangamin yakin neman zabensa a garin Makurdi.

Legit.ng ya ruwaito a ranar Laraba, 6 ga watan Feburairu ne shugaba Buhari ya isa garin Makurdi, babban birnin jahar Benuwe, domin halartar yakin neman zabensa a karo na biyu daya gudana a filin wasa na Aper Aku.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel