Jigo a APC ya ce kowa ya zabi abinda ya ke so bayan zaben Buhari

Jigo a APC ya ce kowa ya zabi abinda ya ke so bayan zaben Buhari

Shugaban ‘yan a ware na jam’iyyar APC reshen jihar Legas, Fouad Oki ya shaidawa magoya bayansa cewa bayan zaben Buhari, suna da damar su zabi wanda suke ko da kuwa ba jam’iyyarsu ta APC bane.

Shugaban ‘yan a ware na jam’iyyar APC reshen jihar Legas ya fadawa magoya bayansa cewa bayan zaben Shugaba Muhammadu Buhari da Farfesa Yemi Osinbajo, suna da damar zaben duk wani dan takara ko da bad an jam’iyyar APC bane.

A wurin yakin neman zaben Shugaban Muhammadu Buhari da aka gudanar a Alimosho a jihar Legas, Fouad Oki ya ce rikicin da ke tsakaninsa da dayan bangaren jam’iyyar yana gaban kotu kuma yana fatan za a warware matsalolin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Jigo a APC ya ce kowa ya zabi abinda ya ke so bayan zaben Buhari

Jigo a APC ya ce kowa ya zabi abinda ya ke so bayan zaben Buhari
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya na kokarin gurgunta gonar Onnoghen - CUPP

Ya ce, “Da farko, dayan bangaren ba suyi tsamanin za suyi tasiri ba. Amma abin mamaki gashi yanzu sai ma kara karfi su keyi. Kuma mun san cewa za muyi nasara a kotu.

“Babu shakka zaben shugaba Muhammadu Buhari da na Farfesa Yemi Osinbajo zai hada kan mu wuri guda.

“Akwai yiwuwar wasu zabukkan za su hada kawunnan mu a nan gaba. Sai dai ya zama dole mu zabi ‘yan jam’iyyar mu da suka fice daga APC saboda bacin rai. Ba za muyi watsi da su ba.

“Wannan na nufin kowa na da damar zaben dan takarar da yak e ra’ayi ba tare da la’akari da banbancin jam’iyya ba; Wannan shine abinda Shugaba Muhammadu Buhari ya fadi a wurin yakin neman zabensa a jihar Imo,” inji Oki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel