Ga jerin abubuwan da Atiku ya fi sha’awa a rayuwarsa

Ga jerin abubuwan da Atiku ya fi sha’awa a rayuwarsa

Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana jerin abubuwan da ya fi sha'awa a duniya a matsayinsa na dan Adam.

Ya bayyana haka ne ta hanyar maudu'in #AskAtikuYourself, wanda ke nufin #KuTambayiAtikuDaKanku.

Ga jerin abubuwan da Atiku ya fi sha’awa a rayuwarsa

Ga jerin abubuwan da Atiku ya fi sha’awa a rayuwarsa
Source: Twitter

Ga abubuwan da aka tambaye shi da amsoshin da ya bayar:

1. Wanne kulob din kwallon kafa ka fi sha'awa? Da yake bayar da amsa, dan takarar na PDP ya ce "Arsenal ne kulob din kwallon kafar da na fi sha'awa."

2. Wanne abinci ka fi sha'awa? Sai yace babu abincin da ya fi kauna kamar shinkafa dafa-duka, yana mai cewa wakokin marigayi Fela Kuti su ne wakokin da ya fi kauna da sha'awar sauraro.

3. Wacce waka ko kida ka fi sha'awa? Sai Atiku Abubakar ya ce lokacin da Fela ke raye, yana yawan halartar wuraren da yake waka.

Sai dai ya ce a yanzu babu mawakin da ya fi kaunar sauraren wakokinsa kamar Davido.

KU KARANTA KUMA: Rubewar tarbiyya da da’a a Najeriya zai ragu in aka zabi shugaba Buhari karo na biyu – Shugabar matan

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sake barota, inda yayi barazanar halaka duk wani dan kasar waje da yayi ma Najeriya katsalandan a yayin babban zaben 2019 dake karatowa, wanda zai gudana a watan Feburairu da watan Maris.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya yi wannan kalamai ne kimanin makonni uku da gwamnatocin kasashen Amurka, Birtaniya, da kungiyar tarayya kasashen Turai suka yi tofin Allah tsine akan gwamnatin Najeriya bisa sallamar tsohon Alkalin Alkalai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel