Da zafinsa: Atiku ya lashi takobin kammala ginin tashar samar da lantarki ta Mambilla

Da zafinsa: Atiku ya lashi takobin kammala ginin tashar samar da lantarki ta Mambilla

- Alhaji Atiku Abubakar, a ranar Talata, ya sha alwashin kammala ginin tashar samar da wutar lantarki ta Mambilla, idan har aka zabe shi a ranar 16 ga watan Fabreru

- Ya ce gwamnati mai ci a yanzu na yiwa aikin tafiyar hawainiya, tare da gazawa wajen biyan hakkokin jama'a da aka karbi filayensu

- Prince Uche Secondus, ya bukaci al'ummar jihar da su zabi jam'iyyar PDP a dukkanin matakan kujerun zabe

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a ranar Talata, ya sha alwashin kammala ginin tashar samar da wutar lantarki ta Mambilla, idan har 'yan Nigeria suka zabe shi a ranar 16 ga watan Fabreru.

Atiku ya sha wannan alwashin a garin Jalingo, jihar Taraba, a yayin kaddamar yakin zabensa.

Ya ce gwamnati mai ci a yanzu na yiwa aikin tafiyar hawainiya, tare da gazawa wajen biyan hakkokin jama'a da aka karbi filayensu, uwa uba kuma gaza kai 'yan kwangila a wurin aikin, inda ya sha alwashin mayar da hankali wajen gina manyan titunan gwamnatin tarayya na jihar.

KARANTA WANNAN: Ba wasa: Igbo, Hausa, Fulani sun sha alwashin tunbuke Buhari ta hanyar zabar Atiku

Da zafinsa: Atiku ya lashi takobin kammala ginin cibiyar samar da lantarki ta Mambilla

Da zafinsa: Atiku ya lashi takobin kammala ginin cibiyar samar da lantarki ta Mambilla
Source: UGC

Ya jaddada bukatar da ke da akwai na jami'an tsaro da su kasance marasa nuna banbanci a lokacin gudanar da ayyukansu, musamman ma a lokacin gudanar da babban zabe na 2019.

Atiku ya bukaci masu kad'a kuri'a a Taraba da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zabarsa a ranar 16 ga watan Fabreru, inda ya sha alwashin samar da ayyukan raya kasa a gare su.

A na shi jawabin a yayin taron, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya bukaci al'ummar jihar da su zabi jam'iyyar PDP a dukkanin matakan kujerun zabe saboda ba su damar samun ayyukanyi, zaman lafiya da kuma habbakar tattalin arzikin kasa da dorewarsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel