Ana yunkurin taka mani burki ne saboda a hana Ibo mulki - Okorocha

Ana yunkurin taka mani burki ne saboda a hana Ibo mulki - Okorocha

Mun samu labari cewa mai girma gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya gargadi mutanen sa game da zaben bana na 2019 inda yace idan ba su yi amfani da kaifin hankalin su ba, za ayi babu su a Najeriya.

Ana yunkurin taka mani burki ne saboda a hana Ibo mulki - Okorocha

Okorocha yana da niyyar sake neman takarar shugaban kasa a 2023
Source: UGC

Jaridar The Nation ta rahoto Rochas Owelle Okorocha yana kira ga Inyamuran kasar nan su zama masu kaifin basira a daidai lokacin da zaben 2019 ya gabato. Gwamnan yace wasu daga wajen Imo ne su ka hura wutan rikicin siyasar jihar.

Rochas Okorocha yace muddin Inyamurai ba su yi wa kan-su karatun ta-natsu ba, za su cigaba da yin kuskure a siyasar Najeriya, inda mutanen na Ibo ke kukan cewa an maida su saniyar ware tun bayan yakin basasa da aka yi a Najeriya.

KU KARANTA: Ibo, Hausa, da Fulani sun sha alwashin zaben Atiku a 2019

Gwamnan wanda ke shirin barin gado yake cewa wasu manyan APC sun huro wuta a hana Surukin sa takarar gwamna ne saboda su yi kokarin ganin an kassara shi a siyasa da kuma burin da Ibo su ke yi na karbar ragamar mulkin kasar nan.

Gwamna Okorocha ya kuma bayyana ainihin dalilin sa na zuwa majalisar dattawa bayan kammala wa’adin sa na gwamna. Okorocha yace yana so ne a cigaba da gwabzawa da shi har zuwa 2023, sannan yace zai nemi takarar shugaban kasa.

Gwamnan na APC yace shugaba Adams Oshiomhole da Rotimi Amaechi sun hana Uche Nwosu tikiti a APC ne saboda su na ganin cewa idan ya kafa gwamna, kuma ya tafi majalisar dattawa, zai yi karfi har ya garare su zuwa zaben 2023.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel