Zamu halaka duk wanda yayi mana katsalandan a zabe – El-Rufai ga yan kasashen waje

Zamu halaka duk wanda yayi mana katsalandan a zabe – El-Rufai ga yan kasashen waje

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sake barota, inda yayi barazanar halaka duk wani dan kasar waje da yayi ma Najeriya katsalandan a yayin babban zaben 2019 dake karatowa, wanda zai gudana a watan Feburairu da watan Maris.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya yi wannan kalamai ne kimanin makonni uku da gwamnatocin kasashen Amurka, Birtaniya, da kungiyar tarayya kasashen Turai suka yi tofin Allah tsine akan gwamnatin Najeriya bisa sallamar tsohon Alkalin Alkalai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.

KU KARANTA: An ci, an sha, and koshi yayin da Buhari ya karbi bakoncin yan majalisa a Villa

Gwamna El-Rufai wanda jigo ne a jam’iyyar APC, kuma dan gani kashenin shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin hira da aka yi da shi a gidan talabijin na kasa. NTA, cikin wani shiri mai taken ‘Tuesday Live’.

“Duk masu kira ga kasashen waje dasu shigo su yi mana katsalandan, toh muna jiran mu ga wanda zai mana katsalandan, sai mun mayar dasu a cikin jakkunan gawa.” Inji Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai.

A cewar El-Rufai, Najeriya kasace mai zaman kanta kuma mai cin gashin kanta, don haka ba zata tankwaro a wajen kasashen waje ba, ya kara da cewa Najeriya na iya bakin kokarinta wajen tafiyar da mulkin dimukradiyyarta, kuma da haka sauran kasashen duniya suka kai ga matsayin da suka kai a yanzu.

Sai dai duk kokarin da jaridar Premium Times ta yi na jin ta bakin kaakakin gwamnatin jahar Kaduna, Samuel Aruwan game da wadannan kalamai na gwamnan jahar ya ci tura, haka zalika Ministan watsa labaru na Najeriya, Lai Mohammed yaki cewa uffan game da wannan magana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel