Dalilin da yasa na dawo daga rakiyan gwamnatin Tambuwal – Tsohon kwamishinan Sokoto

Dalilin da yasa na dawo daga rakiyan gwamnatin Tambuwal – Tsohon kwamishinan Sokoto

A ranar Talata, 5 ga watan Fabrairu ne kwamishinan bayanai na jihar Sokoto, Barista Bello Muhammad Goronyo ya sanar da komawarsa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga Peoples Democratic Party (PDP).

Gwamna Tambuwal ne ya nada tsohon kwamishinan a watan Oktoba na shekarar da ta gabata. Amma sai ya koma tsohuwar jam’iyyar gwamnan a lokacin da take kaddamar da kamfen dinta a mahaifar Shugaban jam’iyya, garin Wamakko, hedkwatar karamar hukumar Wamakko.

Dalilin da yasa na dawo daga rakiyan gwamnatin Tambuwal – Tsohon kwamishinan Sokoto

Dalilin da yasa na dawo daga rakiyan gwamnatin Tambuwal – Tsohon kwamishinan Sokoto
Source: UGC

A wajen taron Goronyo yace: “Na dawo cikin jam’iyar APC, Sanata Wamakko gwanina ne kuma mahaifi da na dogara dashi. Ya kasance mutum mai gaskiya kuma shugaba nagari.

“Yau ran ace mai dauke da tarihi a gare ni, iyalaina da dukkanin abokan siyasa na. Na san cewa na tafka kura-kurai, amma a yafe mani.

KU KARANTA KUMA: Rubewar tarbiyya da da’a a Najeriya zai ragu in aka zabi shugaba Buhari karo na biyu – Shugabar matan APC

“Nayi alkawarin aiki don tabbatar da nasarar yan takarar jam’iyyar, a dukkan matakai a fadin kasar.”

Tsohon ministan sadarwar wanda hya kasance Shugaban kwamitin labarai na PDP, ya bayyana ewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi namijin okari wajen kai kasar Najeriya gaba kamar yadda sanata Wamako yayi tsakanin 2007 sa 2015 lokacin da yakke a matsayin gwamnan jihar Sokoto, cewa hakan ne ya sanya shi koma jam’iyyar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel