Kada ka kuskura ka murkushe kungiyar tsagerun IPOB – Magoya bayan Atiku ga Buratai

Kada ka kuskura ka murkushe kungiyar tsagerun IPOB – Magoya bayan Atiku ga Buratai

Babbar kungiyar kabilar Ibo ta Najeriya, Ohanaeze, babban kungiyar kabilar Yarbawa, Afenifere da kuma kungiyar tuntuba ta Neja Delta, PANDEF sun yi Allah wadai da umarnin da babban hafsan Sojan kasa Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya baiwa Sojoji game da murkushe kungiyar IPOB.

Su dai wadannan kungiyoyi guda uku sune suka bayyana ma duniya goyon bayansu dan takarar jam’iyyar PDP a matakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, yayin da ita kuma kungiyar IPOB dake rajin kafa kasar Biyafara a karkashin jagorancin Nnamdi Kanu tayi kira ga Inyamurai da kada su yi zabe a 2019.

KU KARANTA; Sojoji sun halaka yan bindiga 9, sun ceto mutanen da suka yi garkuwa dasu guda 2 a Zamfara

Kada ka kuskura ka murkushe kungiyar tsagerun IPOB – Magoya bayan Atiku ga Buratai

Tsagerun IPOB
Source: Twitter

Kungiyoyin, Ohanaeze, Afenifere da PANDEF sun bayyana umarnin da Buratai ya bayar a matsayin barazana ne kawai, don haka suka nemi da ya janye wannan umarni, domin kuwa basu bukatarsa a wannan lokaci.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ohanaeze na kira ga rundunar Sojan kasa da kada ta kuskura ta maimaita kuskuren data tafka a shekarar 2017 da sunan “Operation rawar mesa” inda suka kashe mutane tare da lalata dukiyoyi a yankin Inyamurai.

Shugaban kungiyar, Nnia Nwodo ne ya bayyana haka a ranar Talata, 5,ga watan Feburairu, inda yace IPOB ba kungiya bace dake neman tashin hankali, kuma umarnin data baiwa yayanta na kin shiga zaben 2019 ba zai yi tasiri ba, domin bai taba yin tasiri a baya ba.

Bugu da kari, Nwodo ya zargi rundunar Sojan kasa da kulla wata kullalliya da za ta hana al’ummar Inyamurai fita domin kada kuri’unsu a zaben watan Feburairu na 2019, ta hanyar sanya shinge akan hanyoyi da kuma musguna ma jama’a da sunan murkushe IPOB.

Shima kaakakin kungiyar yarbawa ta Afenifere, Yinka Odumakin ya nanata wannan zargi na Ohanaeze, inda yace wannan wani mataki ne da gwamnati ta dauka domin mamaye yankin da ta san APC bata da karfi da Sojoji.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel