Febrairu 16: Jirgin yakin neman zaben Buhari zai dira Legas ranan Asabar

Febrairu 16: Jirgin yakin neman zaben Buhari zai dira Legas ranan Asabar

Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta saki jadawalin yakin neman zabenta na ranan Asabar, inda za ta garzaya babban birnin jihar Legas domin cigaba da gabatar da sakon Nexl Level gabanin zaben da za'ayi na da kwanaki goma.

Jihar Legas ta kasance babbar jihar da jam'iyyar APC tafi yawan mabiya a yankin kudu maso yamma, da akafi sani da yankin Yarbawa.

Ana sa ran cewa duk da karshen mako ne, zuwan Buhari zai jawo cikas wajen sufuri musamman a kwaryar birnin Legas.

Gabanin halartan taron yakin neman zaben, shugaban kasan zai kai ziyarar wurare daban-daban musamman fadar sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, domin gaisuwar ban girma.

KU KARANTA: Wata kyakkyawar mata mai ciki ta damfari Dangote

Mun kawo muku cewa shugaban kasa Muhammadu Buhaeri, a yau Laraba, ya dira filin sauka da tashin jirage na Makurdi, a ziyarar kaddamar da yakin zabensa da ya kai jihar Benue.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa shugaban kasar tare da tawagarsa, sun dira a filin sauka da tashin jiragen ne da misalin karfe 10:45 na safiyar Laraba.

Shugaban kasar ya samu rakiyar manyan shuwagabannin jam'iyyar da kuma gwamnonin da ke makwaftaka da jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel