Rikicin Benuwai: Operation Whirl Stroke sun ceci Mutanen Guma

Rikicin Benuwai: Operation Whirl Stroke sun ceci Mutanen Guma

- Kwanan nan wasu ‘Yan bindiga su ka nemi su kai hari a Benuwai

- Sojojin Najeriya da ke cikin Jihar sun takawa ‘Yan bindigan burki

Rikicin Benuwai: Operation Whirl Stroke sun ceci Mutanen Guma

Dakarun Operation Whirl Stroke sun fatattaki 'Yan bindiga
Source: UGC

Mun samu labari cewa an kai hari a cikin jihar Benuwai da ke cikin tsakiyar Najeriya. Jami’an tsaro sun taimaka wajen ganin an ci karfin wadannan ‘yan bindiga. Ana dai fama da matsalar tsaro yanzu a bangarorin Najeriya.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Daily Trust ta kasar nan a jiya, Rundunar sojin Najeriya ne su ka takawa ‘yan bindigan da su ka kai hari a cikin garin Tse Tseghem da ke cikin Benuwai burki a farkon makon nan.

KU KARANTA: Buhari ya dira cikin Makurdi domin kaddamar da yakin zaben 2019

Dakarun sojin Najeriya na Operation Whirl Stroke watau OPWS su ne su ka fatattaki ‘yan bindigan da su ka yi yunkurin kai farmaki a Tse-Tseghem wanda wani kauye ne da ke cikin karamar hukumar Guma a jihar Benuwai.

Wani babban jami’in Sojan kasa na Najeriya wanda kuma shi ne shugaban Dakarun na OPWS, Manjo Janar Adeyemi Yekini ya bayyanawa ‘yan jarida cewa babu shakka ‘yan bindiga sun nemi su kawo hari a farkon makon nan.

KU KARANTA: Sojoji sun ce 'yan ta'adda ba su mamaye garuruwan Adamawa ba

Janar Adeyemi Yekini yayi wannan jawabi ne a Ranar Talata inda yace Sojojin sa sun hana wadannan ‘yan bindiga shiga yankin Tomator da ke cikin garin na Guma. An yi ta musayar bindiga tsakanin sojojin kasar da ‘yan bindiga.

Babban jami’in sojan bai bada wani karin bayani da ya wuce wannan ba, a lokacin da ya zanta da manema labarai a cikin garin Makurdi, wanda nan ne babban birnin jihar Benuwai. Adeyami yace sojojin sa sun hana ‘yan bindigan kai hari.

Kwanakin baya an ta samun hare-haren ‘yan bindiga a jihar Benuwai da ke cikin Arewa maso tsakiyar Najeriya. An alakanta wannan hare-hare da rikicin da ake yi tsakanin Makiyaya da kuma Manoman jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel