Rubewar tarbiyya da da’a a Najeriya zai ragu in aka zabi shugaba Buhari karo na biyu – Shugabar matan APC

Rubewar tarbiyya da da’a a Najeriya zai ragu in aka zabi shugaba Buhari karo na biyu – Shugabar matan APC

Misis Rachel Akpabio, shugabar mata na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a yankin kudu maso kudu ta bayyana cewa sake zabar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zama tamkar dole domin ceto kasar daga lalacewar tarbiya.

Akpabio ta bayyana hakan a lokacin hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba, 6 ga watan Fabrairu a Port Harcourt.

Ta bayyana cewa saura kiris kasar ta gama fadawa a rikici a fannoni daban-daban kama daga tattalin arziki zuwa tsaro har said a gwamnati mai mulki tayi gaggawan shiga lamarin.

Rubewar tarbiyya da da’a a Najeriya zai ragu in aka zabi shugaba Buhari karo na biyu – Shugabar matan APC

Rubewar tarbiyya da da’a a Najeriya zai ragu in aka zabi shugaba Buhari karo na biyu – Shugabar matan APC
Source: UGC

Shugabar matan ta bayyana ewa wasu yan Najeriya da ke sukar gwamnati mai mulki sun gaza duba tarin alkhairin da tazarcen shugaba Buhari zai kawo.

Ta kara da cewa daga lokacin da Shugaban kasar ya karbi mulki sai ya karanci dukkanin rikice-rikicen da ke barazana ga ci gaban kasar sannan ya fara magancesu ta hanyar da ya dace.

KU KARANTA KUMA: Tsohuwar shugabar kasar Liberia Johnson-Sirleaf ta isa Abuja don zaben 2019

A halin yanzu, mun samu cewa a jiya Talata cikin birnin Awka na jihar Anambra, dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Peter Obi, ya yi karin haske dangane da yadda wasu ke ci gaba da goyon bayan jam'iyya mai ci ta APC.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Dakta Obi ya ce rashin son aminci da samun kyakkyawar makoma matabbaciya a Najeriya ya sanya wasu ke ci gaba da goyon bayan jam'iyya mai ci ta APC.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana hakan ne yayin wani yawon shawagi da ya gudanar cikin jihar sa domin wayar da kan al'umma tare da fadakar wa yayin da babban zaben kasa ya ke daf da gudana a ranar 16 ga watan Fabrairu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel