Babban Sufeton 'yan sanda ya ziyarci shugaban kamfanin man fetur na kasa, Maikanti Baru

Babban Sufeton 'yan sanda ya ziyarci shugaban kamfanin man fetur na kasa, Maikanti Baru

A yayin ci gaba da yunkurin su na sauke nauyin da ya rataya a wuyan su wajen inganta ci gaban kasa ta hanyar tabbatar da zaman lafiya, hukumar 'yan sanda za ta hada gwiwa da babban kamfanin man fetur na kasa wajen yakar masu fasa bututun mai.

Sabon sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu, shine ya bayar da shaidar hakan yayin da ya ziyarci shugaban kamfanin man fetur na kasa, Dakta Maikanti Baru, a ma'aikatar sa da ke garin Abuja.

Babban Sufeton 'yan sanda tare da Maikanti Baru

Babban Sufeton 'yan sanda tare da Maikanti Baru
Source: Twitter

Babban Sufeton 'yan sanda yayin ziyarar kamfanin man fetur na kasa

Babban Sufeton 'yan sanda yayin ziyarar kamfanin man fetur na kasa
Source: Twitter

Sufeto Adamu ya ce hadin gwiwar za ta inganta harkokin tsaro musamman ta fuskar yaki da masu mummunar ta'ada da tsagerancin fasa bututun mai da dukkanin wasu miyagun ababe da suka shafin man fetur da ma'adanan sa a fadin kasar nan.

Domin tabbatar da ingancin dabaru na habaka tattalin arzikin kasar nan, babban jami'in tsaron ya ce kamfanin NNPC ya kasance ma'aikata ta farko da ya ziyarta tun yayin karbar ragamar jagorancin hukumar 'yan sanda a watan da ya gabata.

KARANTA KUMA: Rashin son aminci a Najeriya ya sanya wasu ke goyon bayan Buhari - Peter Obi

Ya ce muhimmancin kamfanin NNPC a kasar nan da ya kasance jigo wajen habakar tattalin arziki ya sanya hukumar 'yan sanda za ta mike tsaye wurjanjan domin tunkarar barazana ta ta'adar fasa bututu da satar man fetur.

Cikin zayyana na sa jawaban, shugaban kamfanin man fetur na kasa, Dakta Baru ya taya murna ga babban jami'in bisa ga nadin sabon mukamin sa tare da gargadin sa akan jajircewa wajen tabbatar da tsaro da kuma rashawa a fadin Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel