Yanzu yanzu: Buhari ya dira Makurdi domin kaddamar da yakin zabensa

Yanzu yanzu: Buhari ya dira Makurdi domin kaddamar da yakin zabensa

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhaeri, a yau Laraba, ya dira filin sauka da tashin jirage na Makurdi, a ziyarar kaddamar da yakin zabensa da ya kai jihar Benue.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa shugaban kasar tare da tawagarsa, sun dira a filin sauka da tashin jiragen ne da misalin karfe 10:45 na safiyar Laraba.

Shugaban kasar ya samu rakiyar manyan shuwagabannin jam'iyyar da kuma gwamnonin da ke makwaftaka da jihar.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Dogara ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, ya kira shi Fir'auna

Yanzu yanzu: Buhari ya dira Makurdi domin kaddamar da yakin zabensa

Yanzu yanzu: Buhari ya dira Makurdi domin kaddamar da yakin zabensa
Source: UGC

Ana sa ran Buhari zai kai ziyarar gaisuwa ga basaraken Tiv, Farfesa James Ayatse da kuma ganawa da gwamna Samuel Ortom a gidan gwamnatin jihar kafin zarcewa babban filin wasanni na Aper Aku, inda zai kaddamar da yakin zaben na sa.

A wani labarin kuma, tuni jami'an tsaro suka kasance a filin da za a kaddamar da yakin zaben, a yayin da magoya bayan jam'iyyar APC ke ci gaba da tururuwa a filin, suna zaman jiran isowar shugaban kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel