Rashin son aminci a Najeriya ya sanya wasu ke goyon bayan Buhari - Peter Obi

Rashin son aminci a Najeriya ya sanya wasu ke goyon bayan Buhari - Peter Obi

Mun samu cewa a jiya Talata cikin birnin Awka na jihar Anambra, dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Peter Obi, ya yi karin haske dangane da yadda wasu ke ci gaba da goyon bayan jam'iyya mai ci ta APC.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Dakta Obi ya ce rashin son aminci da samun kyakkyawar makoma matabbaciya a Najeriya ya sanya wasu ke ci gaba da goyon bayan jam'iyya mai ci ta APC.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana hakan ne yayin wani yawon shawagi da ya gudanar cikin jihar sa domin wayar da kan al'umma tare da fadakar wa yayin da babban zaben kasa ya ke daf da gudana a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Peter Obi yayin taron yakin neman zaben jam'iyyar PDP a jihar Delta

Peter Obi yayin taron yakin neman zaben jam'iyyar PDP a jihar Delta
Source: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa, taron da ya gudana cikin birnin Awka ya yi armashi kwarai da aniyya sakamakon yadda dumbin al'umma mabanbanta juna ta fuskar harkokin rayuwa suka halarta domin wayar ma su da kai dangane da babban zabe.

Kazalika Obi cikin jawaban sa ga dumbin al'umma da suka halarci taron, ya yi kira kan tabbatar da nasarar jam'iyyar PDP a babban zabe ta hanyar jefa kuri'u su ga dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar da ya kasance Atiku Abubakar.

KARANTA KUMA: Mataimakin shugaban kasa zai kaddamar da sabuwar hanyar Layin Dogo daga Ogun zuwa Legas

Ya ce kwarewar Atiku duba da nasarorin sa a baya ka ma daga inganta tattalin arziki zuwa ga tabbatar da kwararar romon dimokuradiyya a kowace yanayi ya sanya ya cancani jagorancin kasar nan domin fidda ita zuwa tudun tsira.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, wata kungiyar magoya baya ta Peter Obi Support Network, POSN, ta sha alwashin samar da kuri'u miliyan goma domin tabbatar da nasarar Atiku a yayin babban zaben kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel