Masu gudun hijira ma zasu dangwala quri'unsu kamar kowa, a sansanoninsu - INEC

Masu gudun hijira ma zasu dangwala quri'unsu kamar kowa, a sansanoninsu - INEC

- Yan gudun hijira dake jihar Borno zasu kada kuri'ar su a sansanin su

- Shugaban hukumar zaben ne ya bayyana haka a shirye shiryen gudanar da zaben da sukeyi

- Kusan mutane 2.3m ne suka karbi katin zaben su

Masu gudun hijira ma zasu dangwala quri'unsu kamar kowa, a sansanoninsu - INEC

Masu gudun hijira ma zasu dangwala quri'unsu kamar kowa, a sansanoninsu - INEC
Source: Depositphotos

Yan gudun hijira dake jihar Borno zasu kada kuri'ar su a sansanin da suke zaune. Haka ma na ko'ina duk za'a kai musu akwatunan zaben har cikin Nijar da Kamaru.

Shugaban hukumar zaben Mohammed Magaji Ibrahim ne ya bayyana hakan a shirye shiryen zaben da zai gudana a ranar 16 Fabrairu shekara ta 2019.

A ranar Laraba kungiyar yan jaridar Najeriya (NUJ) ta bayyana kudirin hukumar zaben akan yan gudun hijirar.

GA WANNAN: Bayan an gano gwamnonin Nijar a taron APC a Kano, Ribadu ya maida martani

"Yan gudun hijira zasu kada kuri'ar su a sansanin da suke zaune,a halin yanzu mun samo sansani da dama wanda Takwas daga cikin su suna wakiltar kananan hukumomi mabambanta".

Ya kara da cewa sama da mutane 2.3m ne suka karbi katin zaben nasu sannan yayi kira a garesu dasu kula da katin nasu duba da cewa hukumar bazata kara bada wani katin ba sai bayan zabe.

Ya bayyana sunayen sansanin da za'a kada kuri'ar banda Kala balge duba da halin da sansanin ke ciki.

Akwai sansanin yan gudun hijira sama da 50 a fadin jihar ta Borno.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel