Biyo bayan alkalumma dake nuna wai Atiku ne zai lashe jihohin tsakiyar Najeriya sun fara yawo, martani daga Nassarawa

Biyo bayan alkalumma dake nuna wai Atiku ne zai lashe jihohin tsakiyar Najeriya sun fara yawo, martani daga Nassarawa

- Kaso 75 cikin 100 na al'ummar jihar Nassarawa zasu zabi Muhammad Buhari

- Balarabe Abdullahi ya tabbatar da hakan a yayin da yake ganawa da manema labarai

- Yayi kira ga yan Najeriya dasu ajjiye wata akida su zabi Buhari

Biyo bayan alkalumma dake nuna wai Atiku ne zai lashe jihohin tsakiyar Najeriya sun fara yawo, martani daga Nassarawa

Biyo bayan alkalumma dake nuna wai Atiku ne zai lashe jihohin tsakiyar Najeriya sun fara yawo, martani daga Nassarawa
Source: Twitter

Dan majalisar tarayya dake wakiltar jihar Nassarawa Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi ya bayyana cewa kaso 75/100 na kuri'un Jihar duk na shugaban kasa Muhammad Buhari ne a zaben da zai gudana a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Balarabe Abdullahi ya bada wannan tabbaci a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan zuwan shugaban kasar jihar Nassarawa gudanar da kamfe.

A bangaren sa yace zuwan shugaban kasar jihar kamar zuwa gidane duba da soyayyar dake tsakani.

"Ina da tabbacin kaso 75 na kuri'un jihar Nassarawa na Muhammad Buhari ne duba da cigaba da aka samu a jihar dama kasa baki data".

GA WANNAN: Yadda duniya tayi asarar $200m, bayan mai gadinsu ya mutu bai fadi lambar sirrin ba

Balarabe Abdullahi ya kara da cewa jihar ta amfana da abubuwa da dama kasancewar Buhari a jam'iyar APC.

Daga karshe ya shawarci yan Najeriya dasu ajjiye akida su zabi Buhari da Osinbajo su kuma tayasu dz addu'ar samun nasara.

Yace Buhari ya ceto kasar mu daga shirin durkushewa da tayi sannan kuma yana da tabbashin zai lashe zaben 16 ga watan nan da muke ciki.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel