Gwamna Nasir da Isa Ashiru sun sanya hannu kan takardan lumana gabanin zabe

Gwamna Nasir da Isa Ashiru sun sanya hannu kan takardan lumana gabanin zabe

- Yan takarar gwamna a APC da PDP a jihar Kaduna sun sanya hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya a zabe mai zuwa

- Sun sanya hannun ne a ranar Talata a hedkwatar hukumar yan sandan jihar

- Sunyi wannan abune dan tabbatar da samun tsaro da kwanciyar hankali a yayin gudanar da zaben

Bayan kashe-kashe da yaransu na siyasa keyi gabanin zabe, an tilasta wa Gwamna Nasir da Isa Ashiru sanya hannu kan lumana

Bayan kashe-kashe da yaransu na siyasa keyi gabanin zabe, an tilasta wa Gwamna Nasir da Isa Ashiru sanya hannu kan lumana
Source: Facebook

A ranar Talata ne gwamnan jihar Kaduna Mal.Nasir El-rufai da dan takarar gwamna a jami'yar PDP Alhaji Isa Ashiru da ragowar yan takara suka sanya hannu akan takaddar zaman lafiya a bisa zaben da zai gudana.

Sunyi hakan ne dan kauda tsoro da hargitsi a jihar da kuma samar da zabe mai inganci.

Duk yan takarar gwamna a jihar ta Kaduna sun sanya hannu a wannan yarjejeni a hedkwatar hukumar yan sandan jihar Kaduna dake Bida road.

Kwanishinan yan sandan jihar Ahmad Abdulrahman yace za'a samu kyakyyawan tsaro a jihar a lokacin zabe da kuma bayan zabe.

GA WANNAN: Bayan an gano gwamnonin Nijar a taron APC a Kano, Ribadu ya maida martani

Ya kara da cewa "ya zama tilas yan takara da magoya bayansu subi tsarin da aka shimfida a maimakon data fitina".

"Mu shirya karbar duk wani sakamako da muka samu kodan kasarmu ta samu zaman lafiya, su kuma wadanda suka samu nasara kar suyi amfani da wannan dama wajen tsokanar abokan hamayyar su".

Da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan sanya hannun dan takarar na jam'iyar PDP yayi kira ga hukumar zabe data sanya ido a duk wani wajen da za'a kada kuri'a.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel