Karin hasken da soji suka bayar kan rahotannin mamaye garuruwan Adamawa

Karin hasken da soji suka bayar kan rahotannin mamaye garuruwan Adamawa

- Ofishin operation lafiya dole na arewa maso gabas ya karyata rahoton da wasu mawallafan yanar gizo ke badawa

- A ranar 4 ga watan nan ne Sahara reporters suka wallafa cewa Boko Haram sun kwace garuruwa hudu a Adamawa

- Yan ta'adda dai sunkai hari kauyen Shuwa amma rundunar sojin sunyi musu kaca kaca

Karin hasken da soji suka bayar kan rahotannin mamaye garuruwan Adamawa

Karin hasken da soji suka bayar kan rahotannin mamaye garuruwan Adamawa
Source: UGC

Ofishin operation lafiya dole na arewa maso gabas ya kwatanta rahoton dake zagaye a yanar gizo na cewa yan ta'addan Boko Haram sun kwace garuruwa hudu a jihar Adamawa da karya.

Mai magana da yawun ofishin, Col. Onyema Nwachukwu, a maganar shi a Maiduguri jiya, yace: "An jawo hankalin ofishin operation lafiya dole akan wani labari mai batarwa da Sahara Reporters suka ruwaito tare da wallafawa a ranar 4 ga watan Fabrairu 2019, na cewa yan ta'addan Boko Haram sun kwace garuruwa 4 a jihar Adamawa,"

"Hakan ba gaskiya bane, akasin abinda Sahara reporters suka ruwaito, ofishin mu na farincikin sanar da mutane cewa wallafar babu gaskiya a cikin ta kuma ko kusa da gaskiya bai kai ba a al'amuran dake faruwa a jihar Adamawa,"

"Babu wani gari a jihohin Adamawa, Borno da Yobe dake karkashin yan ta'addan," inji Col. Nwachukwu.

GA WANNAN: Bayan an gano gwamnonin Nijar a taron APC a Kano, Ribadu ya maida martani

Ya jajanta tare da cewa, "Abin haushin shine, rahoton ya jawo tsoro ga mutane mara dalili kuma akwai bukatar wayar musu da kai akan hakan."

"Akwai dai lokacin da aka sanar da rundunar sojin akan wani hari da Boko Haram suka kaiwa Shuwa har suka shiga kauyen Karchinga da burin sata, wanda Bataliya ta 143 suka maida martani ta hanyar rarraba kansu a kauyen Shuwan. Sunyi ruwan wuta da yan'ta'addan kuma sunyi nasara akan su,"

"Sojin sun samu kwace wasu makamai daga yan ta'addan kuma a halin yanzu suna kauyen shuwa don cigaba da zakulo Yan ta'addan da suka gudu. Abin haushin dai shine kafin isar rundunar, har Yan ta'addan sun kashe mutane 3, sun fasa tare da kwashe wani shago, cibiyar lafiya da kuma kasuwa."

Amma a halin yanzu kauyen shuwa na lafiya,Madagali, Michika, Gulak da Baza suna lafiya kuma karkashin kulara rundunar

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel