Tsohuwar shugabar kasar Liberia Johnson-Sirleaf ta isa Abuja don zaben 2019

Tsohuwar shugabar kasar Liberia Johnson-Sirleaf ta isa Abuja don zaben 2019

- Gabannin zaben 2019 Ellen Johnson-Sirleaf, tsohuwar shugabar kasar Liberia ta iso Abuja don isar da wani aiki

- Johnson-Sirleaf wacce ta iso Najeriya a jiya ta samu tarba daga mataimakin Shugaban ECOWAS, Finda Koroma, mambobin hukumar da kuma wasu wakilan daga majalisar ECOWAS

- A cewar tsohuwar shugabar kasar ta Liberia, tana sanya ran haduwa da shugabannin siyasa sannan ta shiga sahun tabbatar da tsarin zabe na lumana da nasara

Ellen Johnson-Sirleaf, tsohuwar shugabar kasar Liberia, a ranar Talata, 5 ga watan Fabrairu ta iso Abuja a matsayin shugabar masu lura na ECOWAS a Najeriya gabannin zaben 2019.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa ta samu tarba daga mataimakin Shugaban ECOWAS, Finda Koroma, mambobin hukumar da kuma wasu wakilan daga majalisar ECOWAS.

Tsohuwar shugabar kasar ta Liberia tace za ta bayyana binciken kudirin baya da tattaunawa da wadanda suka riga suka iso domin kula da zaben.

Kasa da makonni biyu kafin zaben 2019, kasashen duniya sun rigada sun turo wadanda za su kula da tsarin zabe sosai.

Tsohuwar shugabar kasar Liberia Johnson-Sirleaf ta isa Abuja don zaben 2019

Tsohuwar shugabar kasar Liberia Johnson-Sirleaf ta isa Abuja don zaben 2019
Source: Original

Tsohuwar shugabar kasar ta Liberia ta kuma yi alkawarin cewa za ta tabbatar da tsarin zaben Najeriya cikin kwaciyar hankali da kuma nasara.

KU KARANTA KUMA: Gaskiyar dalili da yasa Oshiomhole da Amaechi ba sa farin ciki da ni – Okorocha

Sirleaf ta yi alkawarin ne yayinda ta samu tarba daga mataimain Shugaban hukumr ECOWAS, Finda Koroma, a filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Ta kuma samu tarba daga mambobin hukumar ECOWAS din da kuma wasu wakilan daga majalisar ECOWAS.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel