Babbar magana: Dogara ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, ya kira shi Fir'auna

Babbar magana: Dogara ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, ya kira shi Fir'auna

- Yakubu Dogara ya fito fili, inda ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, Muhammadu Abdullahi Abubakar, tare da kiransa a matsayin 'Fir'aunan kasar Masar'

- Da ya ke jagorantar wani taro na masu ruwa da tsaki a jihar, Dogara ya yi ikirarin cewa gwamnan ba dan asalin jihar ba ne

- Dogara ya kuma ce lokaci ya yi da shiyyar Arewa maso Gabas za ta rike shugabancin kasar ta hanyar zabar Atiku Abubakar

Kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara ya fito fili, inda ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, Muhammadu Abdullahi Abubakar, tare da kiransa a matsayin 'Fir'aunan kasar Masar' yana mai cewa ya zama wajibi a samu sabuwar gwamnati a jihar, domin gujewa ci gaba da mulki karkashin ikon gwamnati mai ci a yanzu.

Wannan jawabi na Dogara ya zo ne a yayin da gwamnan jihar ke ci gaba da samun matsin lamba a cikin jam'iyyar ta sa ta APC a jihar wanda kuma a baya baya kakakin majalisar ya sha kalubalantar irin gazawar gwamnatin jihar mai ci.

Da ya ke jagorantar wani taro na masu ruwa da tsaki a jihar, Dogara ya yi ikirarin cewa gwamnan ba dan asalin jihar ba ne, wannan ne dalilin da ya sa bai damu da ci gaban jihar ba. A tofa albarkacin bakin jama'a kuwa, da yawa na ganin cewa gwamnan ya fito ne daga kabilar Igbira da ke jihar Kogi, wanda ya samun gindin zama a jihar Bauchi bayan da ya samu aikin gwamnati a farkon karni na 8.

KARANTA WANNAN: Rundunar soji ta karyata cewa Boko Haram ta mamaye garuruwa 4 a Adamawa

Babbar magana: Dogara ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, ya kira shi Fir'auna

Babbar magana: Dogara ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, ya kira shi Fir'auna
Source: UGC

Da ya ke jawabi a taron yakin zaben jam'iyyar PDP a jihar Bauchi, Dogara ya kuma ce lokaci ya yi da shiyyar Arewa maso Gabas za ta rike shugabancin kasar ta hanyar zabar Atiku Abubakar. Ya ce Atiku zai yi aiki tukuru domin kawo ci gaba da hadin kai a kasar.

Da ya ke nuni da irin gazawar gwamnatin jihar karkashin gwamna M.A Abubakar, Dogara ya ce: "A jihar Bauchi ne kadai ake mulki kamar na Fir'auna. To ka sani, idan ma kai Foto kofi ne, munga yadda Allah ya yi da shi ainihin Fir'aunan.

"Zamu kawo wani (Sanata Bala Mohammed) wanda zai dawo da martabar jihar Bauchi. Hakika abun takaici ne yadda za a ce akalla yaranmu 1.3m ne ke zaune a gida basu zuwa makaranta, wanda kuma hakan na nuni da cewa zamu iya fuskantar matsalar tsaron da ta zarce ta yanzu wacce kuma zata bamu ciwon kai wajen magance.

"Ya zama wajibi mu tashi tsaye, mu kori yunwa, talauci, rashin tsaro da kuma mulki irin na Fir'auna," a cewar Dogara.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel