Gaskiyar dalili da yasa Oshiomhole da Amaechi ba sa farin ciki da ni – Okorocha

Gaskiyar dalili da yasa Oshiomhole da Amaechi ba sa farin ciki da ni – Okorocha

- Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha yayi karin haske akan rashin jituwar shi da Adams Oshiomhole da kuma Rotimi Amaechi

- Okorocha yace shugabannin biyu ba sa farin iki dashi ne saboda ya hana su juya jihar Imo yadda suke so a siyasance

- Gwamnan ya ce furucin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin gangamin kamfen din dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar a Imo ya tabbatar da hadin da ke tsakanin Jam’iyyar Action Alliance (AA) da APC

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo, a ranar Talata, 5 ga watan Fabrairu yayi karin haske akan rashin jituwar shi da Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Kwamrad Adams Oshiomhole da kuma ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

A cewar shi, shugabannin biyu ba sa farin iki dashi ne saboda ya hana su juya jihar Imo yadda suke so a siyasance.

Okorocha yayinda yake zantawa da manema a gidan gwamnati a Owerri, yayi ikirarin cewa daga Oshiomhole har Amaechi bayan sun gaza yin nasara a kudirinsu sai suka yanke shawarar marawa Uzodinma baya a matsayin dan takarar gwamna na APC.

Gaskiyar dalili da yasa Oshiomhole da Amaechi ba sa farin ciki da ni – Okorocha

Gaskiyar dalili da yasa Oshiomhole da Amaechi ba sa farin ciki da ni – Okorocha
Source: Depositphotos

Ya ci gaba da cewa furucin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin gangamin kamfen din dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar a Imo ya tabbatar da hadin da ke tsakanin Jam’iyyar Action Alliance (AA) da APC.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram na nan daram dam a garin Baga – Inji ‘yan gudun hijira

Gwamnan ya kuma yi ba a gay an takarar jam’iyyun Peoples Democratic Party (PDP) d All Progressive Grand Alliance (APGA) a jihar inda ya bayyana cewa ba su samu ta bisa ka’ida ba.

Okorocha yace Sanata Samuel Anyanwu ne ya lashe tikitin PDP amma aka ba Cif Emeka Ihedioha, yayinda aka mika na APG ga Ifeanyi Araraume a Abuja d APGA reshen Anambra.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel