2019: Sam bai dace a ba Atiku Abubakar amanar Najeriya ba inji Tinubu

2019: Sam bai dace a ba Atiku Abubakar amanar Najeriya ba inji Tinubu

A jiya ne APC tayi wani babban taro na yakin neman zabe inda manyan jam’iyyar irin su shugaban kasa Muhammadu Buhari; da mataimakin sa Yemi Osinbajo; da kuma Asiwaju Bola Ahmed Tinubu su ka halarta.

2019: Sam bai dace a ba Atiku Abubakar amanar Najeriya ba inji Tinubu

Jam’iyyar APC tayi kaca-kaca da ‘Dan takarar PDP Atiku a Ekiti
Source: Twitter

Manyan na APC sun caccaki ‘dan takarar PDP Atiku Abubakar da kuma tsohon Mai gidan sa Cif Olusegun Obasanjo, wanda su ka zarga da kashe tattalin arzikin kasar nan a lokacin da su kayi mulki na tsawon shekaru 8.

Babban jigon APC Bola Tinubu ya fadawa jama’a a wajen yakinneman zaben cewa ka da su sake su zabi Atiku Abubakar a zaben da za ayi kwanan nan. Tinubu yace idan Atiku ya samu mulki, sata kurum zai tafka ba komai ba.

KU KARANTA: Atiku Abubakar ne zai iya magance matsalolin Najeriya - Peter Obi

Bola Tinubu yace PDP ta na yi wa jama’a alkawarin bogi ne da cewa za su samawa al’umma aikin yi saboda ganin cewa Atiku Abubakar ‘dan kasuwa ne. Tinubu ya nemi jama’a su guji ruduwa da irin wannan maganganu.

Tsohon gwamnan na Legas yace abin da ya kamata a tambayi PDP shi ne mutum nawa su ka samu aikin yi a lokacin da su ke mulki. Tinubu ya kara da zargin cewa sau da-dama gwamnatin Obasanjo tana satar kudi daga asusun PTDF.

Sauran wadanda su ka halarci wannan kamfe sun hada da gwamnoni irin su Kayode Fayemi da Oluwarotimi Akeredolu da kuma Sanata Ayo Fansanmi inda aka yi kira a sake zaben Buhari karo na biyu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel