An gano wata makarkashiyar da hukumar EFCC ta shirya wa korarren alkalin-alkalai

An gano wata makarkashiyar da hukumar EFCC ta shirya wa korarren alkalin-alkalai

Wata kungiya wadda ba ta gwamnati ba mai rajin kare demkradiyya data kunshi gamayyar wasu jam'iyyun siyasa a Najeriya watau Coalition of United Political Parties (CUPP) ta ce ta bankado wasu shiri da hukumar EFCC ke yi na cafke korarren alkalin alkalai, Mai shari'a Walter Onnoghen.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a ta bakin kakakin ta na kasa Mista Imo Ugochinyere wanda ya bayyanawa manema labarai hakan yayin da yake zantawa da su a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

An gano wata makarkashiyar da hukumar EFCC ta shirya wa korarren alkalin-alkalai

An gano wata makarkashiyar da hukumar EFCC ta shirya wa korarren alkalin-alkalai
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Zakzaky ya umurci mabiyan sa su kauracewa zaben 2019

Legit.ng Hausa ta samu cewa Mista Imo Ugochinyere ya kara da cewa wani binciken sirri da suka gudanar, ya tabbatar masu da cewa jami'an na hukumar EFCC sun shirya kai wa shi alkalin alkalan farmaki ranar Laraba da nufin cafke shi.

Haka zalika ya sha alwashin cewa su a matsayin su na kungiya za su yi iya bakin kokarin su wajen ganin hakar su bata cimma ruwa ba domin kuwa sai inda karfin su yakare.

A wani labarin kuma, Shugaban rikon kwarya na hukumar gwamnatin tarayya dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), Ibrahim Magu mun samu labarin cewa ya rubutwa shugaba Muhammadu Buhari takarda game da Mai shari'a Walter Onnoghen.

Kamar yadda muka samu, takardar wadda shugaban na EFCC ya rubutawa Shugaba Buhari a karshen watan da ya gabata wacce ta sirri ce wasu 'yan jaridu sun same ta ne ranar Talata da ta gabata ta hannun wata kungiya mai zaman kan ta ta Coalition of United Political Parties (CUPP).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel