Rundunar soji ta karyata cewa Boko Haram ta mamaye garuruwa 4 a Adamawa

Rundunar soji ta karyata cewa Boko Haram ta mamaye garuruwa 4 a Adamawa

Rundunar soji da ke atisayen LAFIYA DOLE a shiyyar Arewa maso Gabas ta bayyana cewa labarin da ake yadawa na cewar 'yan ta'addan Boko Haram sun mamaye garuruwa hudu a jihar Adamawa karyar banza ce, kuma labari ne da baida tushe. Shafin jaridar Sahara Reporters ne ya fara wallafa labarin a ranar 4 ga watan Fabreru, wanda rundunar sojin ta kira a matsayin 'karya tsagoronta'.

Mai magana da yawun rundunar, Kanal Onyema Nwachukwu, a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Maiduguri a ranar Talata, ya ce: "Rundunar soji da ke atisayen LAFIYA DOLE ta ci karo da wani rahoto da ake yadawa, wanda ya samo asali daga Sahara Reporters da ta wallafa a shafinta a ranar 4 ga watan Fabreru 2019, cewa Boko Haram ta mamaye garuruwa hudu a jihar Adamawa.

"Wannan labarin kanzon kurege ne. Akasin labarin da shafin Sahara Reporters ta wallafa, rundunar sojin na son sanar da daukacin 'yan Nigeria cewa wannan labarin karya ce kawai kuma ya saba da gaskiyar abubuwan da ke faruwa a jihar Adamawa.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Mai tsawatarwa a majalisar dokokin jihar Ekiti ta sauya sheka daga PDP zuwa APC

Ashe duk karya ce: Boko Haram ba ta mamaye garuruwa 4 na Adamawa ba - Rundunar soji

Ashe duk karya ce: Boko Haram ba ta mamaye garuruwa 4 na Adamawa ba - Rundunar soji
Source: Twitter

"Maganar gaskiya, babu wani gari a cikin jihohin Adamawa, Yobe ko Borno da ke karkashin ikon 'yan ta'addan," a cewar Kanal Nwachukwu, yana mai jaddada cewa, "Abun takaici, irin tashin hankalin da wannan labari ya haddasa a cikin al'umma, domin haka ne ya zama wajibi mu dauki mataki.

"Haka zalika muna son sanar da jama'a cewa, hatta garuruwa irin su Shuwa da aka kaiwa hari, suna cikin kwanciyar hankali a yanzu bayan da jami'an rundunarmu suka fatattaki 'yan ta'addan. Haka zalika garuruwa irinsu Madagali, Michika, Gulak da Baza na karkashin ikon rundunar soji, cikin kwanciyar hankali."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel