Da alamu Gwamnonin PDP ba za su kawowa Buhari kuri’a a zaben 2019 ba

Da alamu Gwamnonin PDP ba za su kawowa Buhari kuri’a a zaben 2019 ba

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Vanguard, maganar da ake yi na cewa gwamnonin kudancin Najeriya za su bari jam’iyyar APC mai mulki ta samu kuri’a a zaben bana ya fara rushewa.

Da alamu Gwamnonin PDP ba za su kawowa Buhari kuri’a a zaben 2019 ba

Gwamnonin Kudu sun fara tunanin hana APC ta wawuri kuri'a a zaben bana
Source: Depositphotos

Yarjejeniyar da ake tunani an yi tsakanin jam’iyyar APC da PDP domin ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu akalla kashi 25% na kuri’un da za a samu a kasar Inyamurai yana neman wargajewa a halin yanzu.

Gwamnonin kasar na neman canza shawara ne bayan sun yi wani zama da Atiku Abubakar, wanda shi ne ke rike da tutan PDP na takarar shugaban kasa. Ana rade-radin gwamnonin za su hada kai da APC ne domin su samu su zarce.

A yankin na kudu maso gabas, gwamnoni 3 sun fito ne daga jam’iyyar PDP yayin da jam’iyyar APGA ta ke rike da Anambra a hannun gwamna Willie Obiano, sai kuma jihar Imo inda jam’iyyar APC ke da gwamna Rochas Okorocha.

KU KARANTA: Abin da ya sa na tarawa Buhari Jama’a a Ebonyi – inji Gwamna Umahi

Gwamnaonin PDP na kasar kudun; Dave Umahi, Ebonyi; Ifeanyi Ugwuanyi, Enugu da Okezie Ikpeazu, duk su na kokarin komawa kan kujerun su ne. Gwamnonin sun dade su na nuna cewa babu fada tsakanin su da shugaba Buhari.

Ana tunanin gwamnonin su na tunanin barin shugaba Buhari ya tashi da akalla kashi 25% na kuri’un zaben bana. Sai dai yanzu kamar yadda mu ka samu labari, gwamnonin sun ga matsalar barin hakan ta faru bayan sun zauna da Atiku.

Gwamnonin yankin musamman irin su Dave Umahi wanda ya saba nuna soyayyar sa ga Shugaba Buhari tun yana ANPP ya fara nuna shakkar hada kai da APC a zaben bana saboda rashin farin jinin APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel